Daga Ipole Amajama

Afirka ta sake komawa tsakiyar rikicin siyasar duniya, yayin da matsalar rashin tsaro ke ƙara bazuwa daga yankin Sahel zuwa Najeriya da sauran sassan nahiyar.

Wannan yanayi na barazana ga ƙasashe masu rauni tare da jefa yankuna da dama cikin rashin kwanciyar hankali.

Duk da cewa matsalolin cikin gida, raunin hukumomi da gazawar shugabanci suna taka muhimmiyar rawa wajen haifar da wannan matsala, akwai ƙarin damuwa kan irin tasirin da shigar Rasha ke yi a harkokin Afirka da kuma sakamakon da hakan zai iya haifar wa nahiyar.

Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar ta’addanci wadda ta wuce iyakokinta, yayin da wasu ƙasashen yankin Sahel da ke ƙarƙashin mulkin sojoji suka shiga wani yanayi na rashin tabbas.

Raunin tsarin mulki a waɗannan ƙasashe ya samar da damar da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke amfani da ita wajen ƙara faɗaɗa tasirinsu.

Kalubalen da ake fuskanta a yanzu ba wai kawai batun goyon baya ko adawa da gwamnatocin soja ba ne, sai dai yadda za a magance matsalolin da suka jefa yankin cikin rikici da kuma illolin ware kai daga haɗin gwiwar duniya.

Masu sharhi kan harkokin duniya na ganin cewa shigar Rasha a Afirka na da alaƙa da manyan muradun siyasa, inda Moscow ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta tare da ƙalubalantar ƙasashen Yamma.

Ana zargin cewa maimakon mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa, Rasha na anfani da rikice-rikicen Afirka wajen ƙarfafa matsayinta a siyasar duniya, musamman a lokacin da take fuskantar matsin lamba daga ƙasashen Yamma sakamakon yaƙin Ukraine.

Wannan ya haifar da muhimmiyar tambaya: Shin Rasha ta kasa samar da mafita ga matsalolin Afirka ne, ko kuwa tana amfani da rashin tsaro a matsayin wata hanya ta cimma manufofinta?

Wasu masu nazari na cewa Moscow na iya amfana daga rikice-rikicen Afirka, musamman saboda tasirin da rashin tsaro ke yi ga kasuwannin makamashi da albarkatun ƙasa.

Idan samar da man fetur, iskar gas da ma’adinai a Afirka ya ragu, hakan na iya shafar farashi a kasuwannin duniya.

A gefe guda kuma, Turai na daga cikin wuraren da ke fuskantar babbar matsin lamba sakamakon rikice-rikicen Afirka.

Ƙaruwa da yawan masu gudun hijira daga yankunan da ke fama da tashin hankali na sauya yanayin siyasa a wasu ƙasashen Turai.

Wannan yanayi na ƙara ƙarfafa wasu ƙungiyoyin siyasa masu tsananin ra’ayi, tare da haifar da sabani kan manufofin Turai game da Afirka da kuma yaƙin Ukraine.

A yankin Sahel, shigar Rasha bai kawo gagarumin sauyi wajen magance ta’addanci ko inganta shugabanci ba kamar yadda aka yi tsammani.

Maimakon haka, masu suka na cewa matsalolin tsaro da tattalin arziki sun ci gaba da ƙaruwa a wasu ƙasashen da suka dogara da wannan haɗin gwiwa.

Ko da yake yana da wahala a tantance ko wannan na faruwa ne da gangan ko kuma sakamakon gazawar manufofi, abin da ya bayyana shi ne cewa rashin tsaro a Afirka na ci gaba da ƙara tsanani.

Babban darasin da Afirka za ta koya shi ne cewa bai kamata ta dogara da wani “mai ceto” daga waje ba.

Nahiyar na buƙatar tsayawa da kanta, ƙarfafa hukumomi, da samar da haɗin gwiwa wanda zai ba ta damar kare muradunta.

Dole ƙasashen Afirka su nemi tsarin hulɗa da duniya wanda zai ba su damar yin aiki tare da abokan hulɗa daban-daban ba tare da dogaro da wata ƙasa guda ba.

A ƙarshe, makomar Afirka za ta dogara ne kan yadda za ta iya shawo kan matsalolin cikin gida, ƙarfafa haɗin kai da kuma tabbatar da cewa wahalhalunta ba su zama hanyar ciyar da muradun wasu ƙasashe gaba ba.

Ipole Amajama, mai sharhi kan al’amuran zamantakewa, ya yi wannan rubutun ne daga Abuja, kuma ana iya tuntubarsa ta hanyar: amajamaip@gmail.com.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version