Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana mai ƙarfin 13.92MW, domin samar da ingantacciyar wutar lantarki mai araha ga gidaje, ƙananan sana’o’i, cibiyoyin gwamnati da sauran ayyukan tattalin arziki a jihar.

An ƙaddamar da aikin ne a gundumar Sumsumma da ke yankin rukunin gidajen Waziri Ibrahim a Damaturu, a wani mataki na faɗaɗa damar samun wutar lantarki da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta da ɗorewa a Jihar Yobe.

Aikin wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin 13.92MW na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da haɓaka ci gaban karkara, wanda Gwamna Buni ya bayyana a matsayin muhimmiyar hanyar bunƙasa tattalin arziki da samun ci gaba mai ɗorewa.

Gwamna Buni ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa, tare da tabbatar da cewa al’ummomin karkara sun samu damar cin gajiyar ci gaban tattalin arziki.

Ya kuma sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ganin an samu nasarar aiwatar da Dokar Samar da Wutar Lantarki ta 2023, wadda ta bai wa jihohi damar taka rawa wajen tsara tsare-tsare da ƙa’idojin samar da wutar lantarki a matakin jiha.

Tun da farko, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana aikin a matsayin wata alama ta jajircewar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun samu ingantacciyar wutar lantarki mai araha kuma mai ɗorewa.

Ministan, wanda Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Mamuda Mamman, ya wakilta, ya ce gwamnatin tarayya ta samu gagarumar nasara wajen bunƙasa samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin hasken rana da sauran hanyoyin makamashi mai tsafta.

Shi ma Darakta-Janar na Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara, Abba Abubakar Aliyu, ya ce da zarar an kammala aikin, Yobe za ta kasance cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar da makamashi mai tsafta a Najeriya.

A nasa jawabin na maraba, Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri da Makamashi ta Jihar Yobe, Muhammad Muhammad Bara, ya ce aikin ya nuna jajircewar gwamnatocin tarayya da jihohi wajen faɗaɗa hanyoyin samun makamashi mai tsafta, domin hanzarta ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Aikin, wanda Bankin Duniya ke tallafawa, zai amfani al’ummomi a ƙananan hukumomin Damaturu, Bade, Nguru da Potiskum, a ƙarƙashin sabon shirin sabunta fannin wutar lantarki na gwamnatin Shugaba Tinubu, wanda Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara ke aiwatarwa.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version