Daga: Usman Usman Garba
Sarkin Karaye, Mai Martaba Muhammad Maharaz, ya yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyin masu zaman kansu (NGOs), abokan hulɗar ci gaba, masu taimakon jama’a da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara kaimi wajan tallafin da ake bai wa Ilimin Makiyaya, domin bai wa yara daga al’ummomin makiyaya damar samun ilimi da ya dace da rayuwarsu.
Sarkin ya ce ya kamata a ƙara mayar da hankali kan bukatun ilimi na yaran makiyaya, musamman ta hanyar samar da hanyoyin koyarwa da za su yi la’akari da salon rayuwarsu da kuma yawan ƙaura daga wani wuri zuwa wani.
Ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da shirin yaƙin neman ƙara yawan ɗaliban da za su shiga makaranta na shekarar 2026/2027 a Masarautar Karaye, wanda Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Kano (SUBEB), tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin ta Ƙasa (UBEC), ta shirya.
Ya buƙaci hukumomin gwamnati da abin ya shafa su yi aiki kafada da kafada da hukumomin gargajiya, ƙungiyoyin masu zaman kansu, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin al’umma domin gano yaran da ke zaune a sansanonin makiyaya da tabbatar da cewa sun samu damar zuwa makaranta da samun ingantaccen ilimin da ya dace da bukatunsu.
Haka kuma, Sarkin ya yi kira da a ƙara saka hannun jari a fannin Ilimin Makiyaya, ciki har da samar da kayan koyarwa, ƙwararrun malamai da kuma wuraren koyo da suka dace a yankunan da al’ummomin makiyaya ke zaune.
A cewarsa, ilimi na da matuƙar muhimmanci wajen bai wa yaran makiyaya ilimi da ƙwarewar da za su taimaka musu wajen taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban yankunansu.
Ya kuma buƙaci masu hannu da shuni da sauran masu kishin al’umma da su taimaka wajen cike gibin da gwamnati ba ta iya cikawa, ta hanyar tallafa wa shirye-shiryen ilimi da aka tsara domin yaran makiyaya da sauran al’ummomin da ba sa samun isasshen kulawa.
Sarkin ya kuma yi kira ga iyaye, shugabannin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa dukkan yaran da suka kai shekarun makaranta sun shiga makaranta, sun ci gaba da zuwa, kuma an tallafa musu har zuwa kammala karatunsu na matakin ilimin bai ɗaya.
Ya buƙaci UBEC da SUBEB su ƙara haɗin gwiwa da gwamnatocin jiha da ƙananan hukumomi wajen magance matsalolin da ke hana yaran makiyaya da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta samun ilimi.
Sarkin ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin UBEC da gwamnatocin jihohi domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da buƙatar a tallafa wa makarantun Islamiyya da ilimin zamani.
Ya umarci Hakiman Gundumomi, Dagatai, Masu Unguwanni da Limamai a faɗin Masarautar Karaye da su ba da cikakken goyon baya ga shirin tare da wayar da kan al’ummominsu domin tabbatar da cewa yara sun shiga makaranta kuma sun ci gaba da zuwa har zuwa kammala karatu.
Sarkin ya yabawa UBEC da SUBEB bisa zaɓar Masarautar Karaye a matsayin wurin da aka gudanar da bikin ƙaddamar da shirin, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da goyon baya ga shirin.
Da yake magana a madadin Babban Sakatare na UBEC, Kodinetan UBEC na Jihar Kano, Malam Abdulrahman Musa, ya ce shirin na da nufin wayar da kan iyaye da al’umma domin shigar da yara masu shekaru 6 zuwa 11 makaranta, tare da sauƙaƙa dawowar yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa azuzuwa a dukkan Hukumomin Ilimi na Ƙananan Hukumomi 44 na jihar.
Shi ma Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, wanda Mai Ba Gwamnan Jihar Shawara kan Ilimi, Malam Haladu Muhammad, ya wakilta, ya yi kira ga al’umma, iyaye, shugabannin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu wajen tabbatar da cewa dukkan yaran da ba sa zuwa makaranta sun koma makaranta.
A nata jawabin, Prof. Aisha Abdul Ismail, ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su gano tare da magance matsalolin da ke haddasa yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ta jaddada muhimmancin tabbatar da cewa yaran da aka sanya makaranta sun ci gaba da zuwa har zuwa kammala karatu, tare da yin kira da a ƙara mayar da hankali kan ’yan mata, yara masu nakasa da sauran yara marasa galihu.
A jawabinsa na godiya, Mukaddashin Shugaban SUBEB kuma Kwamishina na I, Hon. Wada Ibrahim Daho, ya yi kira ga iyaye da sauran jama’a da su tallafa wa shirin ta hanyar sanya ’ya’yansu makaranta da kuma tabbatar da cewa sun ci gaba da zuwa har zuwa kammala karatu.
Ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da yake yi wajen inganta harkar ilimi a Jihar Kano, ciki har da gina sababbin makarantu da azuzuwa, gyaran tsofaffin gine-ginen makarantu, samar da kujeru da tebura da kayan koyarwa, da kuma biyan albashi da haɓaka matsayin malamai da ma’aikatan da ba malamai ba a kan lokaci.


