Daga Shuaibu Ibrahim Gusau 

A ƙalla Limamai da Malamai 3,000 daga sassa daban-daban  daga Ƙananan Hukumomi 14 na Jihar Zamfara suka gudanar da addu’o’i na musamman don neman samun dauwamemmen zaman lafiya da samun nasaran Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tunubu a zabe mai zuwa na 2027.

Taron, wanda ya gudana a gidan Darakta Janar na yaƙin yaƙin neman zaben Shugaban ƙasa, Sanata Abdul’aziz Yari, inda aka gudanar da addu’o’in zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ƙasar baki ɗaya, da kuma gudanar da zaɓen 2027 mai zuwa cikin lumana ba tare da rikici ba.

Addu’ar ta fi mayar da hankali ne kan sojojin Nijeriya da sauran jami’an hukumomin tsaro da ke yaƙi da rashin tsaro, domin Allah ya kare su da ya ba su ƙarfi kan dukkan ‘yan ta’adda da ke hana zaman lafiya a ƙasar.

Daga cikin manyan Limamai da suka yi addu’a akwai Sheikh Liman Dan Alhaji daga babban masallacin Gusau. Ya yi addu’ar akan zaɓen 2027 mai zuwa ya gudana cikin lumana, sannan ya roƙi Allah da ya ba shi ƙarin ƙarfi don fatattakar dukkan wakilan shaiɗan da ke shirin haddasa rikicin siyasa da na addini a matsayin makami na rushe zaman lafiya a lokacin zaɓen 2027 mai zuwa.

Haka kuma, wani mashahurin malami, Sheikh Sadiqu Saddeeq, ya yi addu’ar Allah ya ba Sanata Yari damar  gudanar da aikin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi na kamfen din Dawowarsa karo na biyu a mulkin Nageriya.

Sheikh Saddeeq ya ƙara da cewa ya kamata dukan al’umma masu kishin Jihar Zamfara su sani cewa aikin da aka ba Sanata Yari babban ƙalubale ne ba kawai gare shi ba, har ma ga dukan al’umma masu kishin jihar. Ya ce:  “Dukan idanu yanzu nakan  Sanata Yari da jihar.”

A nasa jawabin Sanata Yari ya roƙi malamai da manyan limamai da su cigaba da fadakar da al’umma a Masallatan Juma’a akan kokarin da gwamnatin tarayya keyi akan magance matsalar Tsaro.
Ya ce yanzu haka akwai gagarimin shiri da gwamnatin tarayya keyi na Daukar sojoji wadanda zasuyi aiki a Jihar da sukafito dan magance matsalar tsaron cikin gaggawa.Inji Sanata Yari.

Sanata Yari ya tabbatar da ƙarin kayan Aikin ga Jami’an Tsaro a cikin Jihar zamfara da ƙasa baki ɗaya ya Kuma roki Allah akan duk wanda yake da hannu ko karami ko babban Allah ya tona masa Asiri ya hanashi duk abinda yake nema duniya da lahira.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version