Daga Mahmud Gambo Sani
Sakamakon zaman gaggawar da Majalisar Ƙaramar Hukumar Bichi ta yi da Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar ƙaramar hukumar, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar, dangane da batun ‘yan kasuwa masu ƙorafin jinkirin da aka yi na raba musu shaguna, wanda ya biyo bayan gyara fasalin kasuwar da Ɗanmajalisar Tarayyar na yakin ya yi.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito Shagaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata ya yi alkawarin cewa, duk wanda yake da rumfa a cikin kasuwar zamanin kafin a sabunta ta, zai samu rumfarsa kafin zaɓe mai zuwa da yardar Allah.
Alhaji Hamza Maifata, wanda kuma ya bayyana ganawarsa da ɗan majalisar, bisa irin yadda ya nuna damuwa sosai game da halin da ‘yan kasuwar ke ciki, ya shaida cewa ,dan majalisa Injiniya Abba Bichi, ya janye batun buɗe kasuwar a halin yanzu, kana kuma ya ba da umarnin a fara raba wa ‘yan kasuwar da suke da haƙƙi shagunan da aka kammala gina su.
Baya ga haka, dan majalisar ya umarci lallai a kira ‘yan kwangilar da su ƙara gina wasu shaguna a filin tashar kusa da kasuwar, domin kowa ya samu nasa, wanda a halin yanzu ‘yan kasuwar kowa ya gamsu da makomarsa, sakamakon raba musu shagunan da aka yi a kan tsari.
”Akwai kuma fili da aka ware wanda za a ci gaba da gina shagunan, duk wanda yake da rumfa a kasuwar zai samu rumfarsa, in sha Allahu. Don haka kowa ya yi haƙuri, duba da batu ne da aka fara daga rumfa dubu ɗaya da ɗoriya, amma yanzu an dawo bai fi rumfa ɗari biyu ko ɗari da wani abu ake nema ba.
A hankali wata basirar take zuwa, da iya waɗanda aka gina aka ce a bayar, yau ga shi waɗanda ma aka yi musu irin kwami-kwami ɗin nan, mutane sun buƙaci suna so a ba su, kuma duk an ba su kowa ya mallaka; nasa ne halal-malak! Kawai kuɗin ƙa’ida mutum zai biya ya amsa.”- Alhaji Hamza Sule MaiFata.
Kazalika, ya gode wa ɗaukacin ‘yan kasuwar bisa haɗin kai da suke badawa yadda ya kamata, inda ya tabbatar da cewa da ma akasin da aka samu rashin fahimta da yanayin da ake ciki ne ya haifar da haka. Waɗanda su kuma har yanzu da sauran nasu da ba su ƙara samu ba; su yi haƙuri, su ma nasu suna nan tafe ba da jimawa ba, in sha Allahu kafin zaɓe mai zuwa kowa zai karɓi rumfarsa!” Ya ƙara da wannan.
Alhaji Hamza Sule Maifata, ya kuma jinjina wa dan majalisa Alhaji Abubakar Kabir, bisa ƙoƙarin da ya yi na tsayawa tsayin daka wajen sabunta kasuwar domin gogayya da kowace kasuwa a faɗin Nijeriya.
Trending
- Cross River govt praises journalists for ethical reporting culture
- Cross River Govt applauds journalists for ethical reporting
- Gov. Buni presides over EXCO as Yobe approves ₦59.8bn for key projects
- E-World F.C. triumph in 2026 Federation Cup final
- Adamawa destroys 70 cattle over suspected poisoning, saves hundreds
- Governor Radda empowers 1,169 youths with skills, starter packs
- Sokoto Governor sets up committee to probe market, motor park infernos
- Wamakko’s son, Mahdi, turbaned Yariman Wamakko in Sokoto
