Musa lemu daga Sakkwato.

‎Kotun tarayya da ke zamanta a Sakkwato, ta dage sauraran karan da jam’iyyar ADC ta shigar a gabanta kan wanda zai jagoranci jam’iyyar zuwa ranar 19 ga Mayu 2026.

‎Mai shari’a Ahmad Gama Muhammad wanda ya saurari ƙarar a kan kalubale na wanda zai shugabanci jam’iyyar a jihar Sakkwato.

‎Da yake bayani a gaban kotu, lauyan mai kara, Mista Mathew Burkasa ya bayyana wa kotu cewa , kwace ne aka yi daga wanda ya dace ya shugabanci jam’iyyar a jihar Sakkwato ganin cewa shi ne halaltaccen shugaba.

‎A saboda haka, lauyan mai ƙara, ya tabbatar wa kotu cewa, Wanda yake ƙara shi ne halaltattan shugaban jam’iyyar ADC a jihar.

‎Anan, lauyan ya roki kotu da ta gaggauta yanke hukunci kafin a fara aikin tantance yan takara.

‎Lauyan ya janyo hankalin kotun da ta fahinci cewa , kwace ne aka yi na shugabancin jam’iyyar, da sakataran jam’iyyar wanda hakan ya dace kotun da ta duba domin ba su hakkinsu domin kuwa shugaban da sakataransa, su ne halaltattun shugabannin jam’iyyar ADC a jihar Sakkwato.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version