Daga Usman Usman Garba
Al’ummar unguwar Gobirawa da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano sun yi kira ga ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini, da ya taimaka wajen kammala aikin titin da ya tashi daga Kurna Farin Bene zuwa Babban Layi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa aikin titin, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya fara, bai kammala ba har zuwa yanzu. Sun ce hakan na ci gaba da jefa al’umma cikin wahalhalu, musamman a lokacin damina.
Sun ƙara da cewa titin na da matuƙar muhimmanci ga harkokin sufuri da kasuwanci, kasancewar yana haɗa unguwanni da dama tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da harkokin yau da kullum a yankin Gobirawa da maƙwabtansa.
A cewarsu, sun yanke shawarar yin wannan kira ga Hon. Aliyu Sani Madakin Gini ne saboda irin ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a mazaɓarsa, musamman aikin shimfiɗa tituna a yankin Kurna Yan Ganda, wanda suka ce ya kawo sauƙi da ci gaba ga rayuwar al’umma.
Al’ummar Gobirawa sun bayyana fatan cewa ɗan majalisar zai saurari koken nasu tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kammala aikin titin, wanda za su ce zai taimaka wajen inganta rayuwar jama’a da bunƙasa ci gaban yankin baki ɗaya.
