Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (MOPOL), sun dakile yunkurin da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi na sace dalibai a Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC), Monguno, a Jihar Borno.
Lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 na dare a ranar 19 ga Yuli, 2026.
A halin yanzu, Gwamnatin Jihar Borno na amfani da harabar makarantar FGGC a matsayin masaukin wucin gadi ga daliban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Monguno.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in yada labarai na Hedikwatar Operation Hadin Kai da ke Maiduguri, Kyaftin Mohammed Goni, ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa ‘yan ta’addar sun samu shiga harabar makarantar ne tare da taimakon wasu da ake zargin masu hada baki ne domin aiwatar da shirin sace daliban.
Da jami’an tsaro suka gano harin, nan take suka mayar da martani da bude wa ‘yan ta’addan wuta, yayin da Rundunar 3 Division Quick Reaction Force (QRF) ta isa wurin cikin gaggawa domin karfafa tsaro.
Sakamakon matsin lambar da dakarun tsaro suka yi, ‘yan ta’addar sun tsere cikin rudani ba tare da cimma manufarsu ta sace dalibai ba.
Kyaftin Goni ya ce duk da cewa wasu sassan makarantar sun lalace yayin musayar wuta, jami’an tsaro sun samu nasarar shawo kan lamarin.
Ya kara da cewa bayan harin, an ceto tare da kwashe dalibai 46 zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno, inda aka yi musu gwajin lafiya tare da ba su kulawar da ta dace.
A cewarsa, an tabbatar da cewa dukkan daliban da aka ceto suna cikin koshin lafiya, kuma babu wani dalibi da aka sace.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa cikin takaici, wasu dalibai sun rasa rayukansu sakamakon harbin bindiga da ‘yan ta’addan suka yi yayin harin.
Operation Hadin Kai ta mika ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, tare da tabbatar wa al’umma cewa tana ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi, da kuma tsaron cibiyoyin gwamnati da na ilimi a yankin Arewa maso Gabas, cikin hadin gwiwa da Gwamnatin Jihar Borno.
Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke wadanda ake zargi da hada baki da ‘yan ta’addan, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bibiyar maharan da suka tsere.
Operation Hadin Kai ta sake jaddada kudurinta na ci gaba da matsa wa kungiyoyin ‘yan ta’adda lamba, wargaza karfinsu, hana su gudanar da hare-hare, da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cibiyoyin ilimi da sauran muhimman wurare a yankin Arewa maso Gabas.


