Daga Mu’awuya Bala Idris, Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga bangaren zartarwa da ya dauki matakin gaggawa domin magance matsalar zaizayar kasa da ke barazana ga rayuka da dukiyoyi a garin Kurami da ke Karamar Hukumar Bakori.
Matakin majalisar ya biyo bayan wani kuduri da dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Bakori, Injiniya Abdulrahman Ahmed, ya gabatar a zauren majalisar ranar Talata.
A lokacin da yake gabatar da kudurin, Ahmed ya bayyana cewa ya kawo batun ne a madadin al’ummar garin Kurami, yana mai cewa daukar matakin gaggawa ya zama wajibi domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Ya ce a halin da ake ciki, matsalar zaizayar kasa na ci gaba da yin barazana ga gidaje da sauran kadarorin al’ummar garin, lamarin da ke bukatar daukar matakin gaggawa daga gwamnatin jihar.
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa ya ziyarci garin Kurami, inda ya ga irin girman matsalar, tare da tabbatar da cewa al’ummar yankin na bukatar taimakon gwamnatin jihar cikin gaggawa.
Ahmed ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar da su goyi bayan kudurin domin samun karbuwa daga bangaren zartarwa da kuma tabbatar da daukar matakin da ya dace.
Bayan doguwar tattaunawa kan kudurin, ‘yan majalisar sun nuna goyon bayansu ga kudurin.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Abduljalal Haruna Runka, ya umarci Akawun Majalisar da ya rubuta wa bangaren zartarwa domin sanar da shi amincewar majalisar da kudurin.
Runka ya yaba wa dan majalisar bisa kawo batun gaban majalisar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ceto al’ummar Kurami daga barazanar da zaizayar kasar ke haifarwa.


