Daga Mu’awiya Bala Idris, Katsina
Kungiyar Daura Youth Development Association ta shirya taron addu’a na musamman domin tunawa da kuma neman gafarar Allah ga tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
An gudanar da taron ne a harabar Jami’ar Sufuri ta Daura, wanda ya zo daidai da cika shekara guda da rasuwar marigayin.
Hajiya Aishatu Muhammadu Buhari da Zahra Muhammadu Buhari ne suka wakilci iyalan marigayin a wajen taron addu’ar.
A yayin taron, Liman Ali Aliyu na Gidauniyar Qatar ya jagoranci sauran malamai wajen gudanar da addu’o’in neman gafarar Allah ga Marigayi Muhammadu Buhari.
Haka kuma, Farfesa Salisu Mamman Yanduna ya gabatar da mukala mai taken “Rayuwar Muhammadu Buhari a Matsayin Abin Koyi,” inda ya yi bayani kan rayuwar marigayin da irin darussan da za a koya daga salon shugabancinsa.
A jawabinsa, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana Marigayi Muhammadu Buhari a matsayin shugaba abin koyi, tare da yaba masa kan gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da shugabanci nagari.
Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Faruk Lawal Jobe, ya wakilta, ya ce salon shugabancin Buhari ya kasance abin koyi gare shi wajen tafiyar da mulki bisa gaskiya, riƙon amana da adalci.
Ya kuma yabawa kungiyar Daura Youth Development Association bisa shirya taron addu’ar, tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Marigayi Muhammadu Buhari.
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Zahra Muhammadu Buhari ta gode wa ‘yan Najeriya bisa ci gaba da gudanar da addu’o’i domin mahaifinsu.
Taron ya samu halartar wakilan Mai Martaba Sarkin Katsina da Mai Martaba Sarkin Daura, tare da manyan baki, abokai da masoya na Marigayi Muhammadu Buhari.


