Daga Senator Iroegbu

Taron Africa Forward Summit da aka gudanar a Nairobi, Kenya, ya nuna wata sabuwar alaka tsakanin Afirka da Turai, musamman Faransa.

A karon farko, an gudanar da taron haɗin gwiwar Afirka da Faransa a ƙasar Afirka, inda Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban Kenya William Ruto suka jagoranci taron tare a matsayin abokan hulɗa masu daidaito.

Shekaru da dama, tarurrukan da ke haɗa Afirka da manyan ƙasashen duniya kan kasance a Turai, Amurka, China ko Rasha, inda shugabannin Afirka ke halarta a matsayin masu neman taimako ko tallafi.

Sai dai taron Nairobi ya sauya wannan tsari ta hanyar mayar da hankali kan zuba jari, haɗin gwiwar kasuwanci da samar da kayayyaki a cikin Afirka maimakon dogaro da tallafi.

A yayin taron, an sanar da alkawuran zuba jari da suka kai Yuro biliyan 24, ciki har da biliyan 15 daga Faransa da biliyan 9 daga masu zuba jari na Afirka.

An ware kuɗaɗen ne domin fannoni kamar makamashi, fasahar zamani, noma, lafiya, masana’antu, sufurin ruwa da sauran muhimman sassa.

Marubucin ya jaddada cewa Afirka ba ta rasa albarkatu ko matasa masu ƙwazo, amma tana buƙatar samun damar jari, fasaha da haɗin gwiwar masana’antu cikin adalci.

Saboda haka, mayar da hankali kan samarwa da ƙara darajar kayayyaki a cikin nahiyar na da matuƙar muhimmanci.

A Najeriya, kamfanin otal-otal na Faransa, Accor, tare da Shoreline Group, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zuba jarin dala miliyan 300 domin gina otal-otal 10 a birane takwas kafin shekarar 2030, tare da kafa cibiyar horas da ma’aikatan harkar otal domin samar da ayyukan yi.

Taron ya kuma samar da Africa-France Impact Coalition, wata dandalin kasuwanci da ke haɗa manyan kamfanonin Afirka da Faransa domin haɓaka haɗin gwiwa a fannoni kamar fasahar AI, makamashi mai sabuntawa, noma, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

Sai dai marubucin ya yi gargadin cewa dole ne a tabbatar da aiwatar da alkawuran da aka yi, domin ’yan Afirka sun sha jin irin waɗannan alkawura a baya ba tare da ganin sakamako a ƙasa ba.

Ya kuma bayyana cewa dangantakar Faransa da wasu ƙasashen Afirka, musamman na Yammaci da Tsakiyar Afirka, ta dade tana fuskantar ƙalubale saboda tarihin mulkin mallaka da tsoma baki a harkokin tsaro.

Saboda haka, Afirka ya kamata ta kalli dukkan ƙasashen duniya a matsayin abokan hulɗa na kasuwanci da ci gaba, ba a matsayin masu ceto ko abokan gaba ba.

A cewarsa, idan Faransa da Turai sun rungumi sabon tsarin haɗin gwiwa bisa mutunta juna, zuba jari da bunƙasa masana’antu, hakan zai amfani bangarorin biyu.

Amma nasarar taron za ta auna ne da yawan masana’antu, otal-otal, cibiyoyin bayanai da tashoshin makamashi da za a gina a Afirka cikin shekaru masu zuwa.

Marubucin ya kammala da cewa, idan aka aiwatar da alkawuran da aka yi a Nairobi, to za a iya tuna taron Africa Forward Summit a matsayin lokacin da Afirka ta daina bayyana a matsayin baƙuwa, ta fara tattaunawa da duniya a matsayin abokiyar hulɗa mai cikakken daraja da iko.

 

Senator Iroegbu ɗan jarida ne kuma mai nazari kan tsaro da al’amuran jama’a, za’a iya samunsa ta: senator.iroegbu@yahoo.co.uk.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version