Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Sanata mai wakiltar Mazabar Zamfara ta Yamma kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sakkwato, ya bayar da tallafin tirela 85 na takin zamani ga manoma a faɗin jihar, domin tallafa musu wajen bunƙasa harkokin noma.
A wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, Hon. Ibrahim Muhammad (Danmadamin Birnin Magaji), ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Gusau, an bayyana cewa waɗanda za su ci gajiyar shirin za su biya Naira 20,000 kacal kan kowace buhun taki, yayin da farashin kasuwa ya kai kusan Naira 50,000.
An ce wannan shiri na tallafin taki da Sanata Abdul’aziz Yari ke gudanarwa ba sabon abu ba ne, domin manoma da dama sun dade suna amfana da shi a kowace shekara.
Wani da ya amfana da shirin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ya jima yana cin gajiyar tallafin, yana mai cewa shirin na taimakawa sosai wajen rage wa manoma nauyin kashe kuɗi a lokacin noman damina.
Ya ƙara da cewa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a harkar noma a Jihar Zamfara, akwai buƙatar sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki su yi koyi da irin wannan shiri domin tallafa wa manoma.
A cewarsa, idan aka samu irin wannan tallafi daga bangarori daban-daban, manoman Zamfara za su samu sauƙi matuƙa musamman wajen samar da takin zamani da ake buƙata domin haɓaka amfanin gona.


