Daga Shafi’u Yahaya 

An bayyana kamfanin Crown Flour Mill a matsayin daya daga cikin manyan kamfanonin samar da fulawa da suka fi ba da gudunmawa wajen bunkasa harkokin yin burodi da ci gaban masana’antu a Najeriya.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin daya daga cikin manyan dillalan kamfanin a Kasuwar Singer da ke Kano, Alhaji Umar Buba, Shugaban rukunin kamfanonin Umar Buba Enterprises.

Alhaji Umar Buba ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Burodi ta Kano da kamfanin Crown Flour Mill ya shirya a Kano.

A cewarsa, kamfanin ya nuna jajircewarsa wajen tallafa wa masu sana’ar burodi ta hanyoyi daban-daban.

Ya ce a lokacin taron, kamfanin ya bai wa Kungiyar masu Yin Burodi ta Jihar Kano sabuwar mota kirar bus a matsayin gudunmawa domin saukaka ayyukansu.

Haka kuma, kamfanin ya raba kyaututtuka daban-daban ga gidajen burodi da suka cancanta saboda gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban sana’ar.

Alhaji Umar Buba ya kara da cewa su ma a matsayinsu na manyan dillalan kamfanin sun bayar da gudunmawar buhunan fulawa 150 ga kungiyar domin tallafa mata wajen gudanar da ayyukanta da kuma karfafa dangantaka tsakanin kamfanin da masu sana’ar burodi.

Ya yaba da kokarin Crown Flour Mill wajen inganta harkokin kasuwanci da samar da kayayyaki masu inganci, tare da kira ga sauran kamfanoni da su yi koyi da irin wannan tallafi ga kungiyoyi da masana’antu domin bunkasa tattalin arziki.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version