Daga Mahmud Gambo Sani
Bisa gabatowar zaɓuɓɓukan shekara ta 2027, cibiyar yan jarida ta kasa da kasa watau (International Press Centre- IPC) da haɗin gwiwar Kungiyar Tarayyar Turai (EU) taron bita kan samin makamar aiki da inganta rahotanni kan zaɓen 2027 ga yan jarida a jihar Kano.
Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin 9 ga Nuwamba, 2026, ya sami halartar yan jarida fiye da 40 waɗanda suka fito daga mabambantan kafofin yada labarai da suka haɗa da; gidajen jaridu da gidajen rediyo da telebijin da kuma kafofin sadarwa na zamani.
Da yake jawabin maraba, Daraktan zartarwa na cibiyar, Dokta Lanre Arogundade, wanda shugaban sashen kula da kafofin sadarwa na zamani, Abiodun Adeleke ya gabatar, ya bayyana cewa, kafafen yada labarai suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen karfafa mulkin demukradiyya ta hanyar samar wa yan kasa sahihan bayanai da kuma kiyaye muradun jama’a kafin zaɓe da lokacin zabe da kuma bayan zaɓe.
Ya kuma hori mahalarta bitar da su riƙa musayar bayanai da kuma shawarwari kan yadda za a inganta bayar da rahotannin zaɓe masu inganci a kafofin yada labarai baki daya.
Ya bayyana cewa, bitar za ta sami nasara ne kawai idan har mahalartan suka yi aiki da abin da suka koya wajen bayar da sahihan labarai da kuma da kuma binciken gaskiya kan harkokin zaben 2027 da kuma bayyana wa al’umma ba tare da jin tsoro ko nuna bambanci ba, da kuma kiyaye sahihanci da ɗa’a wajen gabatar da rahotanninsu.
Da suke gabatar da makala a wajen bitar, Dokta Riƙayya Aliyu daga jami’ar Bayero, Kano da Olusola Oludiran daga kungiyar (National Democratic Report – NDR) sun bukaci mahalarta bitar da su rinka zurfafa bincike kan alkawuran da yan siyasa ke yi a lokacin kamfen.
Sun bukace su da su tabbatar da sahihancin rahotanninsu yadda ya kamata, lura da yadda fasahohin zamani suka cika harkar yada labarai da abubuwa na karya wadanda suke da bukatar kyakkyawan binciken tabbatar da sahihancin su.
Daga karshe sun bukaci mahalartan da su tabbatar suna nazartar dokokin kasa na kafafen yada labarai kan rahotannin zaɓe domin samar da ingantaccen rahoto da kuma kauce wa saɓa wa ka’ida wajen gudanar da ayyukansu .
Mahalartan sun bayyana gamsuwarsu bisa gabatar da bitar, inda suka ce, bitar ta zo a kan gaɓa.
Sun yi alwashin ɗabbaka abin da suka koya a lokacin gudanar da ayyukansu.
Trending
- Babban zabe a 2027: IPC,EU sun shirya wa ‘yan-jarida bitar kaifafa basira
- Kano Governor presents N1.107 trillion 2027 budget, prioritises capital development
- Kano allocates 30% of 2027 budget to education, prioritises human capital development
- IPAC to tour 18 Cross River LGAs for governance assessment, announces peace walk …council plans statewide political stakeholders’ conference ahead of 2027 elections
- Alia cautions against political violence, urges issue-based campaigns
- Blue Economy can create millions of jobs for Nigerian youth ~ Sani …says coastal communities could become hubs of employment, food security, wealth creation
- Adamawa to convert fresh air buses to CNG, electric vehicles, orders closure of illegal parks
- Minister suspended broadcast licence fee reviews


