Daga Shuaibu Ibrahim, Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara, ta hannun Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Tallafawa, ta sake jaddada kudirinta na samar da yanayi mai kyau domin gudanar da ayyukan jin kai a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, ya fitar ranar Alhamis a Gusau, ya bayyana cewa ma’aikatar ta himmatu wajen karfafa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin inganta jin dadin al’ummomin da matsalar rashin tsaro ta shafa.
Ya ce hakan ya biyo bayan taron daidaita ayyukan bangaren jin kai na watan Yuli 2026, wanda ya hada kungiyoyin jin kai, kungiyoyin ci gaba da sauran manyan masu ruwa da tsaki domin duba ci gaban ayyukan jin kai da kuma inganta hadin kai.
Sanarwar ta ce an gudanar da taron ne domin gabatar da Rahoton Halin Jin Kai na watan Yuli 2026 tare da bayyana sabbin bayanai kan ayyukan da abokan aikin jin kai ke gudanarwa a jihar.
Da yake gabatar da jawabin bude taron, Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Tallafawa, Hon. Salisu Musa Tsafe, wanda Babban Sakatare mai riko na ma’aikatar, Mrs. Ummulkhairi Abubakar Usman, ta wakilta, ya yaba wa kungiyoyin jin kai bisa kokarin da suke yi wajen tallafa wa al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin ci gaba da hadin gwiwa, musayar bayanai cikin lokaci da kuma tsara ayyuka tare tsakanin gwamnatin jihar da masu gudanar da ayyukan jin kai domin samun ingantaccen sakamako.


