Daga Ahmad Ibrahim Gusau

A wani sabon hari, ‘yan bindiga sun kashe mutane 21 a ƙauyen Bunkasau da ke yankin Zarummai a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.

‎An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen Bunkasau a babura tare da harbe-harbe kan mazauna yankin.

‎Maharan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama, galibinsu mata da yara, tare da kwashe dabbobi a yankin.
‎Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun isa ƙauyen ne a daren Juma’a dauke da makamai na zamani.

‎“Abin takaici ne, da safe ranar Asabar muka tashi muka ga mutane da yawa an kashe su. Akalla mutane 21 aka kashe, kuma har yanzu muna neman wasu da ba a gano ba; sun gudu daga gidajensu sakamakon harin.”

‎A cewarsa, an yi jana’izar mutane 21, inda aka binne su a kabari guda a wata al’umma makwabta.

‎“Don Allah, cikin kuka muna roƙon hukumomi, musamman na jiha da na tarayya, su turo ƙarin jami’an tsaro a yankinmu.”

‎Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa har yanzu ba a tantance adadin waɗanda aka kashe ba.

‎Ya ƙara da cewa rundunar ta tura ƙarin jami’ai domin shawo kan lamarin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version