Daga Mu’awuya Bala Idris, Katsina

Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Katsina (KTIRS) ta fara aikin binciken takardun babura da motoci a fadin jihar domin tabbatar da bin doka da oda tare da kara inganta harkokin tsaro.

Shugaban hukumar, Alhaji Muhammad Isyaku, ne ya kaddamar da aikin a kofar Soro, inda ya bayyana cewa binciken wani bangare ne na ayyukan hukumar da ake gudanarwa domin tabbatar da sahihancin takardun ababen hawa da kuma kara kudaden shiga ga gwamnatin jihar.

Ya ce aikin zai gudana ne na tsawon kwanaki biyar, kuma zai ratsa sassa daban-daban na jihar.

“Wannan bincike yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro, domin gano sahihan bayanan masu ababen hawa tare da taimakawa gwamnati wajen samun karin kudaden shiga,” in ji Isyaku.

Shugaban KTIRS ya bayyana cewa hukumar ta hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki, musamman jami’an tsaro, domin gudanar da aikin cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

Ya kuma yi kira ga masu babura da motoci da su bayar da cikakken hadin kai domin ganin an kammala aikin cikin sauki.

Alhaji Muhammad Isyaku ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar wajen gudanar da ayyukanta.

Haka kuma, ya jinjinawa jami’an tsaro bisa hadin gwiwar da suke bai wa hukumar domin samun nasarar aikin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa irin wannan binciken takardun ababen hawa ana gudanar da shi duk shekara a jihar Katsina tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda, hukumar kiyaye hadurra da sauran jami’an tsaro.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version