Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da Masana’antar Hakar Ma’adinai da Sarrafa Lithium ta Zamfara, wadda aka gina kan jarin dala miliyan 200 a Kauyen Boko, Karamar Hukumar Zurmi.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da masana’antar a ranar Asabar, Gwamna Lawal ya jaddada cewa ana samun ci gaba mai dorewa ne idan aka sarrafa albarkatun kasa cikin gaskiya da rikon amana, tare da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari domin gudanar da ayyukansu cikin alhaki.
Masana’antar, wadda aka kafa ta hanyar hadin gwiwa tsakanin ZAM Mining Company Ltd, Bima Mines Ltd, Jinlide Mining Co. Ltd da sauran abokan hulda, na daga cikin manyan jarin da aka zuba a bangaren ma’adinai a jihar.
Gwamna Lawal ya bayyana kaddamar da masana’antar a matsayin wani muhimmin mataki na cin gajiyar dimbin albarkatun ma’adinai da Allah ya hore wa jihar, ta hanyar bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da amfani mai dorewa da albarkatun kasa.
“Na tsawon shekaru, an san jiharmu a ciki da wajen kasar nan a matsayin wuri mai dimbin ma’adanai. Kasarmu albarkacciya ce, amma girman wannan albarka ya dogara ne kan yadda za mu sarrafa ta cikin alhaki domin inganta rayuwar al’ummarmu,” in ji shi.
Gwamnan ya ce tun daga farkon gwamnatinsa, an dauki kudurin sauya fasalin harkar ma’adinai a Zamfara daga rashin tsari zuwa tsarin da zai samar da daraja da wadata ga al’umma.
Ya kara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa sauye-sauyen da za su inganta harkar hakar ma’adinai bisa doka, jawo masu zuba jari masu nagarta da kuma karfafa hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da cewa bangaren ma’adinai yana bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban tattalin arziki.
“Tattalin arzikin duniya yana sauyawa cikin sauri. Lithium da sauran muhimman ma’adanai su ne ginshikin makomar makamashi mai sabuntawa, motocin lantarki, fasahar zamani da ci gaban masana’antu.
“Jihar Zamfara ba za ta ci gaba da zama wurin samar da danyen ma’adinai kawai ba. Dole ne mu taka rawa a dukkan matakan sarrafawa da samar da kayayyaki,” in ji Gwamna Lawal.
Ya bayyana cewa kafa masana’antar na daga cikin hangen nesan gwamnatinsa na wuce hakar ma’adinai kawai zuwa sarrafa su a cikin gida, kara musu daraja, koyar da sana’o’i da bunkasa masana’antu.
Gwamnan ya tabbatar wa masu zuba jari cewa Gwamnatin Jihar Zamfara za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau domin gudanar da harkokin kasuwanci, ta hanyar karfafa tsaro, inganta ababen more rayuwa da samar da manufofin da za su tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar tabbatar da cewa ayyukan hakar ma’adinai suna mutunta doka, kare muhalli da kuma samar da anfani kai tsaye ga al’ummomin da ake gudanar da ayyukan.
Da yake magana kan al’ummar Kauyen Boko da kewaye, Gwamna Lawal ya ce dole ne su kasance cikin wadanda za su fara cin gajiyar wannan babban jari.
Saboda haka, ya umarci masu gudanar da masana’antar da su ba da fifiko ga daukar ’yan asalin yankin aiki, koyar da sana’o’i, bunkasa al’umma, kare muhalli da kuma gudanar da ayyukan jin kai a matsayin wani bangare na alhakin kamfani ga al’umma.
“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara, ina taya dukkan masu ruwa da tsaki murna bisa wannan gagarumar nasara.
“Yanzu abin alfahari ne a gare ni na kaddamar da Masana’antar Hakar Ma’adinai da Sarrafa Lithium ta Zamfara,” in ji Gwamna Lawal.
