Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, psc+, mnips, ya mika wa gwamnatin jihar Zamfara shanu 329 da tumaki 277 da rundunar ta kwato daga hannun ‘yan fashi da masu satar dabbobi a sassan jihar.
An gudanar da bikin mika dabbobin ne a ranar 20 ga watan Yuni, 2026, inda Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Malam Mani Malam Mummuni (Masaman Mudi, Matawale Bukuyum), ya karbe su a madadin gwamnatin jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar wa manema labarai a Gusau, ya ce an samu nasarar kwato dabbobin ne sakamakon ayyukan sirri da hadin gwiwar ‘yan sanda, sauran hukumomin tsaro da al’umma.
Da yake jawabi, CP Ahmad Muhammad Bello ya bayyana cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyuka domin kawo karshen ‘yan fashi, satar shanu, garkuwa da mutane da sauran laifuka a fadin jihar.
Ya yabawa shugabannin al’umma da mazauna yankunan bisa goyon baya da hadin gwiwar da suke bai wa jami’an tsaro, yana mai cewa samun nasarar aikin tsaro na bukatar musayar bayanai masu inganci da hadin kai.
A nasa bangaren, shugaban al’umma daga karamar hukumar Gummi, Alhaji Abubakar Abdullahi Bargaja, ya bayyana cewa kawo yanzu an kwato sama da shanu 1,500 da aka mayar wa masu su.
Ya kara da cewa inganta tsaro ya taimaka wajen dawo da sama da ‘yan gudun hijira 10,000 zuwa garuruwansu na asali.
Shugabannin al’umma sun yabawa rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki kan kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya.


