Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Yobe ta sanar da fara rajistar maniyyatan aikin Hajjin shekarar 2027, tare da sanya kudin ajiya na farko da ya kai Naira miliyan 7.5 ga duk mai son zuwa aikin Hajjin.
Shugaban Hukumar, Alhaji Mai Aliyu Usman, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Damaturu.
Ya ce watanni uku kacal suka rage kafin a rufe rajistar maniyyatan Hajjin 2027, inda ya bayyana cewa bisa umarnin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da kuma hukumomin Saudiyya, za a rufe rajistar a watan Satumban 2026.
Alhaji Mai Aliyu ya bayyana cewa duk mai niyyar gudanar da aikin Hajjin 2027 dole ne ya bi tsarin da aka tanada na biyan kudin ajiya ta hanyoyin hukuma kawai.
Ya ce ana karɓar kuɗaɗen ne ta hedikwatar hukumar da kuma jami’an karɓar kuɗin Hajji da aka tantance a ƙananan hukumomi.
Ya gargadi jama’a da su guji bai wa mutane ko kungiyoyin da ba su da izinin hukumar kuɗi da sunan za su sauƙaƙa musu tafiyar Hajji, yana mai cewa duk wanda aka kama da irin wannan zamba zai fuskanci hukuncin doka.
Shugaban hukumar ya kuma yi bayanin cewa kuɗin aikin Hajjin 2027 na ƙarshe ba lallai ne su kasance daidai da na shekarar 2026 ba, domin har yanzu ana jiran sanarwar hukumomin Saudiyya da Hukumar Alhazai ta Kasa game da cikakken kuɗin aikin Hajjin na shekarar.
Hakazalika, ya shawarci maniyyatan da fasfofinsu na ƙasashen waje ke dab da ƙarewa da su gaggauta sabunta su domin kauce wa jinkiri ko matsaloli wajen samun bizar tafiya.
Ya kuma umarci jami’an hukumar da ke faɗin jihar su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a da kuma tabbatar da cewa duk masu niyyar zuwa Hajji sun kammala rajistarsu kafin wa’adin rufewa.
A ƙarshe, Alhaji Mai Aliyu Usman ya miƙa godiyarsa ga Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, CON, bisa irin goyon baya da haɗin kan da gwamnatin jihar ke bai wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai wajen gudanar da ayyukanta.


