Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Bayan kisan Jamilu Sani Jangebe, Daraktan Tsare-tsare na Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, da Kansilan Mazabar Jangebe, Hon. Muslim Jangebe, wasu ’yan bindiga sun yi barazanar kashe duk wanda suka kama daga garin Jangebe.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, Hon. Yahaya Yari, ne ya bayyana hakan yayin da yake jajanta wa iyalan mamatan tare da tabbatar da aukuwar lamarin.
A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun bayyana cewa ba su da niyyar sakin duk wanda ya fito daga Jangebe, ko da an biya kuɗin fansa.
“Sun gaya mana cewa duk wanda ya shiga hannunsu matuƙar daga garin Jangebe yake, ba sa son kuɗin fansa. Za su kashe shi ne kawai,” in ji shugaban ƙaramar hukumar.
Ya bayyana cewa hukumomin ƙaramar hukumar sun yi iya ƙoƙarinsu wajen yin sulhu da tattaunawa domin ceto waɗanda abin ya shafa, amma hakan bai yi nasara ba.
Hon. Yahaya Yari ya yi addu’ar Allah Ya jikansa mamatan tare da bai wa iyalansu da al’ummar Jangebe baki ɗaya ƙarfin jure wannan babban rashi.
Haka kuma, ya bai wa mazauna yankin tabbacin cewa gwamnati za ta ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da kamo waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Marigayi Jamilu Sani Jangebe na aiki ne a matsayin Daraktan Tsare-tsare na Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, yayin da marigayi Hon. Muslim Jangebe yake wakiltar Mazabar Jangebe a majalisar ƙaramar hukumar.
Lamarin na daga cikin hare-hare da sace-sacen mutane da suka addabi jihar Zamfara a baya-bayan nan, inda al’ummomin karkara ke ci gaba da rayuwa cikin fargaba da mawuyacin hali sakamakon ayyukan ’yan bindiga masu ɗauke da makamai.

