Daga Usman Usman Garba
Al’ummar Jihar Kano sun bayyana matuƙar jin daɗinsu tare da yabawa ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, bisa matakin gaggawa da ƙwarewa da suka ɗauka wajen dakatar da shirin gudanar da Hawan Sallah na Eid Durbar da masu takarar kujerar Emirancin Kano biyu suka shirya yi.
Shirin gudanar da Hawan Daushe da Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Muhammadu Sanusi II suka shirya ya haddasa fargaba da tashin hankali a tsakanin al’ummar jihar, inda mutane da dama suka nuna damuwa cewa lamarin na iya rikidewa zuwa mummunar tarzoma da za ta iya salwantar da rayukan bayin Allah tare da lalata dukiyoyi masu yawa.
Masana harkokin tsaro da masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa gudanar da hawa biyu a lokaci guda na iya haddasa rikici da tashin hankali a wasu sassan birnin Kano.
Sai dai matakin da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Darakta Janar na DSS da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano suka ɗauka na dakatar da bukukuwan Durbar ya samu karɓuwa sosai, inda aka bayyana shi a matsayin mataki na kishin ƙasa da jarumtaka domin tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da kuma tabbatar da doka da oda a faɗin jihar.
Da take magana kan lamarin, Shugabar Ƙungiyar Lauyoyin Mata ta Women Lawyers Congress, Barrista Nafisa Abba Isma’eel, ta yaba wa jami’an tsaron bisa gaggawar da suka yi wajen dakile yiwuwar rikici.
“Matakin gaggawa da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Darakta Janar na DSS da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano suka ɗauka ya ceci Kano daga wata babbar masifa da ka iya afkuwa.
“Matakinsu ya nuna ƙwarewa, kishin ƙasa da kuma kulawa ta gaskiya ga lafiyar al’umma.
“Muna yaba musu ƙwarai da gaske bisa fifita zaman lafiya da tsaron jama’a sama da komai,” in ji ta.
Barrista Nafisa ta kuma buƙaci al’ummar Kano da su kasance masu bin doka, zaman lafiya tare da mara baya ga duk wani mataki na doka da ake ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Shi ma da yake nasa jawabin, lauya kuma shugaban Kano Concern Civil Society Organisation, Barrista Abubakar Musa Tudun Wada, ya yaba da nuna dattako da sanin ya kamata da sarakunan biyu suka yi wajen bin umarnin jami’an tsaro duk da cewa sun riga sun kammala shirye-shiryen gudanar da hawan.
“Muna matuƙar yaba wa Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Muhammadu Sanusi II bisa nuna haƙuri da girmama hukumomin tsaro ta hanyar dakatar da Hawan Daushe duk da shirye-shiryen da aka riga aka kammala.
Wannan mataki nasu ya taimaka sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da hana tashin hankali mara amfani a Kano,” in ji shi.
Barrista Abubakar Tudun Wada ya ƙara da cewa matakin da sarakunan biyu suka ɗauka babban sadaukarwa ne domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Jihar Kano.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bin doka, su guji duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
Masu sa ido kan al’amura sun bayyana cewa yadda aka warware lamarin cikin lumana tare da dakatar da Hawan Durbar ya sake nuna muhimmancin tattaunawa, nuna dattako da shugabanci nagari wajen kare haɗin kai da zaman lafiyar Jihar Kano.

