Daga Mahmud Gambo Sani 

‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar wa mazauna birnin Kano cewa, matsalar ƙarancin ruwan sha mai tsafta za ta zamo tarihi cikin ‘yan watanni masu zuwa, yayin da gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen gyara tsarin samar da ruwan.

‎Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci ne yayin ziyarar duba aiki da ya kai cibiyar samar da ruwa ta Challawa da ke Panshekara a ƙaramar hukumar Kumbotso, a ranar Laraba.

‎Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar.

‎Gwamnan ya fara duba cibiyoyin tace ruwa tun ranar Talata, inda ya fara da ziyartar gidan ruwa na Tamburawa.

‎A yayin ziyarar, Gwamna Yusuf ya nuna damuwa ganin ɗaya daga cikin manyan layukan famfon ruwa guda uku a halin yanzu ya lalace.

‎Ya kuma tabbatar da cewa, sabon kamfanin da aka ɗauka domin gyara cibiyar tace ruwan zai fara gyaran gaggawa nan ba da jimawa ba, domin a dawo da tura ruwa zuwa birnin, bayan kammala binciken yiwuwar aikin da kuma cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu.

‎Gwamnan ya bayyana cewa kamfanin da aka ba aikin gyaran cibiyar sananne ne a duniya, kuma ya yi alƙawarin yin iya ƙoƙarinsa wajen magance matsalar ƙarancin ruwa nan gaba kaɗan.

‎Ya jaddada cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin gyara manyan cibiyoyin tace ruwa guda biyu a birnin, duk da cewa ƙarfin da suke da shi a yanzu ka iya kasa magance matsalar gaba ɗaya, la’akari da yawan al’ummar jihar da ya haura miliyan 20.

‎“Lokacin da aka fara gina cibiyar ruwan Challawa a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, yawan al’ummar Kano kusan miliyan uku ne,” in ji gwamnan, yana mai jaddada buƙatar faɗaɗa ƙarfin da ake da shi a yanzu domin biyan bukatun zamani.

‎Gwamnan ya yaba wa ma’aikatan cibiyar tace ruwan, bisa jajircewarsu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da mara wa manufofin gwamnati baya wajen kawo ƙarshen ƙarancin ruwa.

‎Ya ƙara da cewa ziyarar ta ba shi damar ganin halin da cibiyar ke ciki da idonsa, wanda hakan zai taimaka wajen tsara ingantacciyar hanya ta gyaran.

‎A halin yanzu, cibiyar ruwan Challawa tana aiki ne da ƙasa da kashi 40 cikin 100 na cikakken ƙarfinta.

‎Gwamna Yusuf ya samu rakiyar Kwamishinan Muhalli (mai kula da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa), Kwamishinan Ilimi, Kwamishinan Ayyuka, da kuma Kwamishinan Wutar Lantarki yayin ziyarar.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version