Daga Mahmud Gambo Sani
A kokarin tabbatar da cikakken tsaro, sahin wayar da kai na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, karkashin jagorancin Darakta Alhaji Sani Anas, na sanar da al’umma cewa, hukumar ta shirya tsaf tare da daukar dukkan matakan da suka dace domin bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyi daga ibtila’in gobara da sauran hadura.
A sanarwar da mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya sanya wa hannu, sanarwar ta ce, hukumar na jan hankalin masu sayar da iskar gas da gidajen man fetur da masu kantuna da filazozi da kamfanoni da kananan masana’antu da asibitoci da makarantu masu zaman kansu da kuma sauran al’umma da su gaggauta zuwa su yi rijista ko su sabunta rigistarsu a hukumar domin tabbatar da ƙa’idojin tsaro da kuma samun agajin gaggawa.
Hukumar ta bayyana cewa, rashin bin wannan umarni na iya jawo asarar rayuka ko dukiya.
Hukumar na ci gaba da jajircewa wajen wayar da kai da kuma kare al’umma baki ɗaya.
Trending
- Babban zabe a 2027: IPC,EU sun shirya wa ‘yan-jarida bitar kaifafa basira
- Kano Governor presents N1.107 trillion 2027 budget, prioritises capital development
- Kano allocates 30% of 2027 budget to education, prioritises human capital development
- IPAC to tour 18 Cross River LGAs for governance assessment, announces peace walk …council plans statewide political stakeholders’ conference ahead of 2027 elections
- Alia cautions against political violence, urges issue-based campaigns
- Blue Economy can create millions of jobs for Nigerian youth ~ Sani …says coastal communities could become hubs of employment, food security, wealth creation
- Adamawa to convert fresh air buses to CNG, electric vehicles, orders closure of illegal parks
- Minister suspended broadcast licence fee reviews


