Daga Mahmud Gambo Sani 

‎A kokarin tabbatar da cikakken tsaro, sahin wayar da kai na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, karkashin jagorancin Darakta Alhaji Sani Anas, na sanar da al’umma cewa, hukumar ta shirya tsaf tare da daukar dukkan matakan da suka dace domin bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyi daga ibtila’in gobara da sauran hadura.

‎A sanarwar da mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya sanya wa hannu, sanarwar ta ce, hukumar na jan hankalin masu sayar da iskar gas da gidajen man fetur da masu kantuna da filazozi da kamfanoni da kananan masana’antu da asibitoci da makarantu masu zaman kansu da kuma sauran al’umma da su gaggauta zuwa su yi rijista ko su sabunta rigistarsu a hukumar domin tabbatar da ƙa’idojin tsaro da kuma samun agajin gaggawa.

‎Hukumar ta bayyana cewa, rashin bin wannan umarni na iya jawo asarar rayuka ko dukiya.

‎Hukumar na ci gaba da jajircewa wajen wayar da kai da kuma kare al’umma baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version