Daga Usman Usman Garba

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi Federal Constituency kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya bai wa kowanne daga cikin alhazan Ƙaramar Hukumar Bichi su 193 kyautar dala 300, kwatankwacin Naira 420,000 domin tallafa musu wajen gudanar da aikin Hajjin bana.

Hon. Bichi ya bayar da tallafin ne yayin da ya kai ziyara ga alhazan a Minna ranar Alhamis, inda suke gudanar da wani bangare na ibadun Hajji.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Hon. Bichi ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin al’adarsa ta shekara-shekara na taimakawa alhazan mazabarsa domin su gudanar da aikin Hajji cikin sauki da walwala.

Jimillar kudin da aka raba ga alhazan 193 ya kai N81,060,000.

Ya kuma bukaci alhazan da su kasance masu da’a tare da zama jakadu nagari na Bichi, Jihar Kano da Najeriya baki daya a lokacin zamansu a kasa mai tsarki.

Hakazalika, dan majalisar ya roki alhazan da su yi addu’o’in zaman lafiya, hadin kai, cigaba da wadata ga Najeriya yayin gudanar da ibadar Hajji.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version