Daga Umar Danladi Ado

Dan Majalisar Dattijai Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke Wakiltar Yankin Sakkwato ta Gabas ya Razana Kwaran da gaske kan labarin rasuwar Sarkin Gobir, Alhaji Isah Muhammad Bawa wanda ya rasu a hannu ‘Yan bindiga.

Ranar labara aka tashi da zancen rasuwar Sarki kafin akai kuɗin fansar da aka yi matsaya za a bayar don a saki Sarkin Gobir din tare da dansa Mai suna Kabiru.

Sanata Lamido ya bayyana rasuwar Sarkin Gobir da cewar wata musiba ce da ta shafi yankinsu gaba daya, ba za su zuba ido wannan lamarin ya tafi a hakan ba.

Ya baiwa dukkan al’ummar Gobirawa a duk in da suke da su yi hakuri ina ba su tabbacin jinin Sarkin Gobir ba zai tafi a banza ba.

Sanata ya yi kira ga gwamnati jiha da tarayya da su sauya tsarin kawar da matsalar tsaro musamman a yankin Sakkwato ta Gabas.

Yace ya kamata gwamnatocin su rika aiki tare da ‘yan majalisar tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a wuraren da suke zaune.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version