Daga Umar Danladi Ado
Hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta Jihar Kebbi SUBEB ta yi kira ga kafafen yada labarai da cewar su yi watsi da dukkanin wasu bayanai dake nuna cewa ba ta karbi Naira Biliyan 1. 39 daga Hukumar UBEB.
Akwai wasu rahotannin dake cewa Jihar Kebbi na cikin wasu jihohi 4 daga yankin arewa maso yamma waɗanda ba su biya kudaden haɗaka da Hukumar UBEB ba.
Shugaban hukumar ta jihar Kebbi Farfesa Suleman Khalid ya bayyana cewar rahoton da Ofishin wasu kafafen yada labarai suka wallafa ba gaskiya bane, inda yace tuni mai girma Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Nasiru Idris ya bayar da umarnin biyan kuɗin hadakar, domin ba Jihar cikakkiyar damar samun kudaden ta.
“Rahoton dake bayanin cewa an hana gwamnatin Jihar Kebbi samun kudin ta na haɗaka na ₦1.39 Billion daga UBEB ba gaskiya bane, Gwamnan jihar Nasiru Idris ya amince da biyan kudin hadakar, kuma gwamnatin Kebbi ta samu karbar kudaden nata, saboda haka babu wasu kudade da hukumar UBEB ta riƙe mata.
“Muna sanar da jama’a cewa N1.39 Billion da aka ambata a cikin rahoton, na cikin kasafin kudi da gwamnatin tarayya ta aike wa hukumar bai ɗaya ta tarayya (UBE) a shekarar 2023, wanda ake rarraba shi ga kowace jiha cikin Jihohi 36 har da Birnin tarayya Abuja.
“Doka ta bayyana cewar gwamnatocin jihohi za su bayar da kuɗaɗe na haɗaka domin samun dama ga kuɗaɗen na Hukumar ta tarayya. A shekarar 2023 kuɗaɗen haɗaka da jihar Kebbi ta buƙata ya kai ₦1,395, 784, 959.51
“Muna kira ga dukkanin bangarorin jama’a kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka mana da wajen sa ido wajen ganin tabbatuwar wannan shiri, shigar su cikin tsarin zai taimaka mana matuka wajen inganta fannin binciken Ilimi a faɗin jihar.
“Mu a hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar jihar Kebbi babban burin mu shine kowane Yaro a Jihar Kebbi ya samu ingantaccen Ilimi, kuma za mu yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin hakar mu ta cimma ruwa.”