Daga Mu’awiya Bala Idris, Katsina

Hukumar Samar da Hanyoyin Karkara da Bunƙasa Kasuwancin Amfanin Gona ta Jihar Katsina (RAAMP) ta gudanar da taron bita kan ƙa’idojin hanya, wanda ya haɗa direbobi, masu amfani da hanyoyi da kuma makarantu domin ƙara wayar da kai kan muhimmancin kiyaye dokokin hanya.

Da yake jawabin buɗe taron, shugaban shirin RAAMP na Jihar Katsina, Engr. Yusuf Yahaya, ya bayyana farin cikinsa da gudanar da taron, tare da miƙa godiyarsa ga mahalarta taron bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa shirin.

Ya ce manufar shirin ita ce bunƙasa hanyoyin karkara da inganta harkokin sufuri, tare da rage haɗurran hanya da asarar rayuka da dukiyoyi da ke faruwa sakamakon rashin bin ƙa’idojin hanya.

A cewarsa, taron bitar zai taimaka matuƙa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin hanya.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Raya Yankunan Karkara da Kyautata Ci Gaban Al’umma, Farfesa Abdulhamid Ahmad, ya yaba wa masu shirya taron, yana mai cewa lokacin damina na buƙatar a ƙara mai da hankali kan harkokin zirga-zirga saboda ƙalubalen da ake fuskanta a hanyoyi.

Ya bayyana cewa taron ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa, sannan ya yi maraba da mahalarta taron da suka fito daga sassa daban-daban na jihar.

Haka kuma, ya shawarce su da su maida hankali wajen koyon darussan da za su amfanar da su da al’ummominsu.

Da yake jawabi a wajen taron, wakilin shugaban shirin RAAMP na ƙasa, Mista Ekum Ojogu, ya gode wa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), hukumar RAAMP da sauran hukumomin da suka bayar da gudummawa wajen tabbatar da nasarar shirin.

Shi kuwa jami’in tuntuba kan ayyukan kiyaye haɗurra, Engr. Okwudili N. Ikejiani, ya gabatar da muhimman bayanai kan ƙa’idojin tuki, dokokin hanya da hanyoyin da direbobi da masu ababen hawa za su bi wajen kare rayuka da lafiyar masu amfani da hanyoyin mota.

Ya jaddada muhimmancin bin dokokin hanya domin rage yawan haɗurra da tabbatar da tsaron duk masu amfani da hanyoyi.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version