Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala shirye shirye ta domin gudanar da bikin cikarta shekaru Talatin da Kafuwa.
Da yake jawabi ga manema labarai a yau sakataren gwamnatin Jihar Zamfara Alhaji Abubakar Nakwada ya ce.”Shirye-shiryen bikin cikarsu shekara 30 za su fara ne a gobe Alhamis 1 ga Oktoba a harabar Baje Kolin Kasuwanci da ke Gusau, sannan kuma za a yi liyafar cin abincin dare ta jihar da yamma.” Inji shi
A cewarsa, ayyukan za su ci gaba a ranar 2 ga Oktoba tare da kaddamar da Block C da aka gyara na rukunin sakatariyar J.B. Yakubu da kuma Masallacin Juma’a na Malam Sambo Dan-Ashafa (Yar Dole) da aka sake gyarawa, wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, da tsohon mai kula da mulkin soja na Zamfara za su kaddamar.
SSG din ya ce, a ranar 3 ga Oktoba, za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki wanda zai hada dukkan tsoffin gwamnonin Zamfara, mataimakansu, da dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya koka da cewa, Zamfara a ahekara 30 ba wai kawai kirga shekaru ba ne game da hada shekaru talatin na tarihi ne da wani sabon tsari na sauyi.
Ya ce, shekaru 27 na farko sun kafa matakai daban-daban na tushen Jihar, shekaru ukun da suka gabata sun yi kokarin karfafa wadannan tushe, da fuskantar gibin ci gaba da aka tara, karfafa tsaro da cibiyoyin gwamnati, sake gina ababen gina dan Adam, farfado da aikin noma, bude sabbin damammakin tattalin arziki da kuma hanzarta zuba jari da zai iya sake mayar da Zamfara gaba a cikin shekaru masu zuwa.
“Abu ne mai matukar muhimmanci cewa yayin da Zamfara ke cika shekaru 30, jiragen kasuwanci za su fara shigowa babban birninta. Ba wai muna murnar nisan da Zamfara ta yi ba ne kawai; muna tabbatar da tsaron al’ummominmu, da mayar da manoma gonakinsu, da zamanantar da aikin noma, da mayar da yara zuwa makarantu mafi kyau.
A cewar Nakwada, karfafa kiwon lafiya, zamanantar da gwamnati, bude sabbin hanyoyi, bude darajar albarkatun kasa da muke da su da kuma samar da sabbin damammaki na inda Zamfara za ta iya zuwa.
“Yayin da muke girmama tarihinmu, babban nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne na gaba don tabbatar da cewa gyare-gyare, ababen more rayuwa, cibiyoyi da jarin da ake kafawa a yau sun zama damammaki masu dorewa da ingantacciyar rayuwa ga tsararraki masu zuwa.
“Zamfara a shekaru 30 saboda haka bikin tarihinmu ne, nuni ne na sauye-sauye da ke gudana, da kuma sabon kuduri na gina Zamfara mafi aminci, wadatar abinci, ilimi, lafiya, hadin kai, mai albarka, mai hadewa, mai amfani da fasahar zamani da wadata a cikin shekaru 30 masu zuwa.
“Muna gayyatar manema labarai, da al’ummar Jihar Zamfara baki daya da su shiga ciki kuma su ba wa wadannan ayyuka na tarihi muhimmancin da ya dace, Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da albarkantar Jihar Zamfara da al’ummarta,” Ya kammala.


