Daga Mahmud Gambo Sani
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai ɗalibai fiye da 600 daga makarantun firamare da ke mazaɓu 11 da ke ƙaramar hukumar, saboda yadda suke zuwa makaranta da kuma jajircewa a kan harkokin karatunsu, ciki har da ɗaliba Khadija Usman daga makarantar Firamare ta Badume wadda ta samu kyautar keken da za ta riƙa zuwa makaranta.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta ƙaramar hukumar Bichi Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta sanya wa hannu ta ce, sauran waɗanda aka karrama sun haɗar da; Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar, Alhaji Bashir Ishaq Muhammad, wanda aka ba shi kyautar babur da kuma Shugaban Makarantar Firamare ta Lawan Shehu, Malam Faruq Abdullahi, da ya rabauta da naira dubu ɗari biyu, sai kuma wani malamin Makarantar Firamare ta Hagagawa, Malam Muhammad Bello da shi ma aka karrama shi sakamakon fice da ya yi a harkar koyarwa.
Shugaban Majalisar yankin, Alhaji Hamza Suleiman Maifata ya kuma samar da mota ƙirar Sharon ga Sashen Ilimi na ƙaramar hukumar.
An kuma karrama malamai fiye da 60 da suka yi fice wajen koyar da darusan lissafi da turanci da kuma ilimin masu buƙata ta musamman daga makarantu daban-daban a faɗin yankin.
Da ya ke jawabi a wajen taron karramawar, Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, wanda ɗan majalisar dokoki na Jiha mai wakiltar Bichi, Alhaji Lawan Shehu ya wakilta, ya ce, an fito da tsarin ne domin zaburar da ɗalibai da malamai da sauran ma’aikatan sashen Ilimi domin su ƙara jajircewa a kan harkokin koyo da koyarwa a makarantun yankin.
”Wannan lokaci kuma a wannan rana, sakamakon ƙwazo da nazarin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi, Honarabul Hamza Sule Maifata, Alhamdu lillahi ya samu yabo kuma mu ma muna yaba masa a ɓangaren hidimta wa ilimi da babu kamarsa, domin babu wata ingantacciyar rayuwa face sai an samar da ilimi ko na addini ko na zamani a cikinta.
Sannan muna da ɗa nmajalisar Tarayya Abubakar Kabiru Abubakar wanda shi ma ya yi fice a jihar Kano da ƙasa baki daya ta fuskar gina al’umma.” Alhaji Lawan Shehu.
Tun da fari a jawabensu daban-daban, Kansilan Ilimi na ƙaramar hukumar, Malam Muhammad Fa’iz Sa’idu da kuma Shugaban Ƙungiyar Malamai ta ƙasa reshen karamar hukumar, Malam Sunusi Ibrahim Bichi, sun taya waɗanda aka karrama murna tare da shawartar sauran ɗalibai da malamai da su yi koyi da su dan ganin cewa su ma sun ci gajiyar irin wannan karramawar a nan gaba.
A nasa ɓangaren, Sakataren Ilimi na yankin, Bashir Ishaq, gode wa ƙaramar hukumar ya yi bisa wannan karramawa da ta yi musu tare da bayyana cewar al’amarin zai taimaka wajen kara bunƙasa harkokin ilimi a yankin.
“Wannan muhimmin taro ne wanda muka samu ƙarfin gwiwar yinsa daga ɓangaren jajirtaccen Shugaban ƙaramar hukumarmu, Alhaji Hamza Sule Maifata wanda yake ba mu gudunmawar da ba mu san yadda za mu yi masa godiya ba, face haɗa masa irin waɗannan tarurrukan masu alfanu.” Alhaji Bashir Ishaq Muhammad.
Taron karramawar ya samu halartar shugabannin makarantu daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkokin ilimi a kafatanin yankin.
Trending
- Yobe Security Council commends peaceful primaries, warns against political violence
- Namadi Dala distributes motorcycles to loyalists
- Sokoto upgrades, renames college after Wamakko
- A Zamfara: Majalisar dokoki ta tsawaita wa’adin dakatar da ‘ya’yanta 7
- Ƙaramar hukumar Bichi ta karrama ɗalibai da jami’an ilimin yankin
- A Bichi: Abubakar Kabir Abubakar ya ciri tuta a zaɓen fitar da gwani
- Cross River cleric condemns Obubra communal clash, alleges over 50 killed
- 2027: Governor Yusuf backs Abba Bichi’s re-election bid
