Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Ministan Tsaro na Kasa, Bello Matawalle, ya taya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, murnar sake nada shi a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
Shugaba Bola Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban kasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayun 2026.
Sakon taya murnar Matawalle ya biyo bayan sanarwar da Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) na APC ya fitar, inda ya tabbatar da Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaba Tinubu a zaben 2027, lamarin da ya kawo karshen hasashe da aka dade ana yi kan tikitin shugaban kasar na jam’iyyar.
Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa sake zaben Shettima shawara ce mai kyau da ta dace, wadda ta samu goyon bayan mambobi da masu ruwa da tsaki na APC.
Ya ce matakin da Shugaba Tinubu ya dauka ya nuna cikakken amincewarsa da Shettima, tare da la’akari da kwarewarsa, hazakarsa, amincinsa da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa ga gwamnati da ci gaban kasa.
“A gare ni da kuma mafi yawan shugabanni, masu ruwa da tsaki da mambobin APC, wannan ita ce mafi dacewa kuma mafi kyawun shawara a wannan lokaci,” in ji Matawalle.
Ya kuma sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a kaddamar da kungiyar “The Tinubu Again Movement”, wadda ya ce shi ne ya assasa domin hada kan ‘yan Najeriya daga dukkan jihohi da shiyyoyin siyasa shida na kasar nan don mara wa tikitin Tinubu/Shettima baya a zaben 2027.
A cewarsa, kungiyar za ta kasance wata kafa ta bayyana nasarorin gwamnatin Renewed Hope, tare da karfafa yakin neman zaben sake dawo da gwamnatin Tinubu da Shettima.
Matawalle ya nuna cikakken yakininsa cewa tikitin Tinubu/Shettima zai sake samun goyon bayan mafi yawan ‘yan Najeriya a babban zaben 2027.
A karshe, ya yi wa Mataimakin Shugaban Kasa addu’ar Allah Ya ba shi karin lafiya, hikima da jagora domin ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tabbatar da ci gaba, zaman lafiya da walwalar al’umma.

