Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ce ta samu rahoton laifuka 145 tare da cafke mutane 240 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tun daga watan Yuli zuwa yanzu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Jibrin Kanfani, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Damaturu.
Ya ce daga cikin laifukan da aka samu akwai kisan kai 16, fyade 9, garkuwa da mutane 1, kwacen dukiya 2, fashi da makami 5, da kuma wasu laifuka 112.
CP Jibrin ya ce sakamakon bincike da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu, an samu hukunci kan mutane 198, yayin da wasu shari’o’i biyu suka samu nasara.
Ya ƙara da cewa, shari’o’i 26 suna gaban kotu, yayin da 10 ke ci gaba da bincike, sannan wasu hudu ke jiran shawarar lauyoyi.
Kwamishinan ya ce nasarorin sun samo asali ne daga ƙoƙarin rundunar na ƙarfafa bincike, gurfanar da masu laifi da kuma ɗaukar matakan da suka dace kan masu aikata laifuka.
Dangane da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi, CP Jibrin ya ce jami’an rundunar sun kama mutane 171 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwato wasu abubuwa da aka haramta da makamai.
Ya kuma bayyana wasu nasarori da rundunar ta samu, ciki har da kama wani da ake zargi da harbin bindiga a Fika, da kuma cafke wani da ake zargi da shigowa daga Maiduguri da nufin satar motoci.
A wani lamari daban, rundunar ta ce ta kama wani da ake zargi da zamba da karkatar da Naira miliyan 77, yayin da jami’an suka kuma cafke wasu mutane biyu da ake zargi da karɓar kuɗi daga wasu mutane bisa tilas.
CP Jibrin ya ce rundunar ta kuma samu ci gaba wajen binciken laifukan da suka shafi sace yara da kisan kai, inda aka kama wasu da ake zargi, aka gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta ƙwarewar jami’ai, hanzarta mayar da martani ga laifuka da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da al’umma.
An rufe taron ne da nuna wasu daga cikin waɗanda ake zargi tare da makamai da sauran kayayyakin da rundunar ta ce ta kwato daga hannunsu.

