Daga Saminu Abdullahi
A bisa nagartar kishi da ƙwazon gina al’umma da Alhaji Abubakar Kabir Abubakar ya sa a gaba, ta sa ya sake zama halastaccen ɗantakar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi, a yayin gudanar da zaɓen fid da gwani na ‘yan takarar majalisar wakilai ta Tarayyar, wanda gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci gudanarwa a Asabar ɗin nan a garin Bichi.
A sanarwar da Jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta sanya wa hannu ta ce, a lokacin ƙaddamar da ɗantakarar, gwamna Abba Kabir Yusuf yana tare da wakilin gwamnatin Tarayya kuma mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara a kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari da kuma wasu daga cikin ‘yan Majalisar Wakilan ƙasar nan.
Da suke jawabi, gwamna Abba Kabir Yusuf da mai ba Shugaban ƙasa Shawara a kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, sun bayyana ɗan majalisar a matsayin jajirtaccen wakili wanda ya mai da hankali wajen hidimta wa al’ummarsa.
Sun kuma bayyana buƙatar da ke akwai na al’ummar ƙaramar hukumar Bichi, da su ci gaba da bai wa ɗan majalisar haɗin kai da goyon baya a kan ya ci gaba da aiwatar da ayyukan da yake yi na alheri a yankin da jiha da ma kasa baki daya.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da takarar tasa, karo na uku, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya bayyana godiyarsa ga Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf da ‘ya’yan Jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar tare da dukkanin al’ummar ƙaramar hukumar Bichi bisa wannan dama da suka sake ba shi na sake komawa zauren majalisar wakilan ƙasar nan.
”Dukkan mutanen da suke wajen wannan gangamin taro iya zunzurutun jama’ar Bichi ne masu albarka da suke ba mu haɗin kai da goyon baya tare da gudunmawa; muna godiya Allah ya saka muku da alheri. Kuma kamar yadda aka yi zaɓe a wannan wuri na mazaɓu 11, Ina so na tabbatar cewa; ni Abubakar Kabiru Abubakar Bichi, na yarda na amince in shiga wannan takara a madadin Jam’iyyar APC mai albarka a zaɓen da za a yi na shekarar 2027.”
A nasa ɓangaren, Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya bayyana godiya ga ɗan majalisar dangane da irin ayyukan alheri da yake gudanarwa a faɗin yankin, tare da ba da tabbacin za su ci gaba da ba shi haɗin kai da goyon baya a dukkan al’amuran da ya sa a gaba, inda daga bisani kuma ya gode wa gwamnatin jiha.
”Allah cikin ikonsa da taimakonsa da taimakon gwamna, ƙaramar hukumar Bichi yanzu ta zama abin misali. Yanayin yadda garin yake yau dole mu gode wa Allah mu gode wa al’umma, musamman mai girma gwamna bisa yadda ya zabi ƙaramar hukumarmu ta Bichi tare da ɗan majalisarmu na Tarayya da yake so ya zo a yi zaben nan a gabansa, wanda daga matakin kasa ma muka samu wakilcin mai bai wa Shugaban kasa Shawara a kan Harkokin Siyasa.” Alhaji Hamza Sule Maifata.
Trending
- Yobe Security Council commends peaceful primaries, warns against political violence
- Namadi Dala distributes motorcycles to loyalists
- Sokoto upgrades, renames college after Wamakko
- A Zamfara: Majalisar dokoki ta tsawaita wa’adin dakatar da ‘ya’yanta 7
- Ƙaramar hukumar Bichi ta karrama ɗalibai da jami’an ilimin yankin
- A Bichi: Abubakar Kabir Abubakar ya ciri tuta a zaɓen fitar da gwani
- Cross River cleric condemns Obubra communal clash, alleges over 50 killed
- 2027: Governor Yusuf backs Abba Bichi’s re-election bid
