Musa lemu daga Sakkwato.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sakkwato a lokacin mulkin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Malam Manir Muhammad Dan’iya, ya bayyana godiyarsa ga Aminu Tambuwal, da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC tare da magoya bayan jam’iyyar bisa ba shi dama domin tsayawa takara a jam’iyyar ADC a zaben 2027.
A cikin takarda da aka raba ga kafofin yada labari na jihar Sakkwato, dauke da sanya hannun tsohon sakataren yada labari na fadar tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abubakar Abdullahi, ya ce, tsohon mataimakin gwamna zai rungumi wannan nauyin da jama’ar jihar suka daura masa a bisa aiwatar da gaskiya da adalci da kamanta gaskiya.
A saboda haka, yayi kira ga magoya bayansa, da jam’iyyar ta ADC da su ba shi hadin kai domin cimma nasara a zabe mai zuwa na 2027.
Dantakarar ya ce, nuna wannan karamci a gare shi da al’ummar Sakkwatawa suka yi hakan zai kara ba shi kwarin gwiwa wajen aiwatar da gaskiya, adalci da amana da zarar ya kasance gwamnan jihar Sakkwato a shekarar 2027.
Jam’iyyar ta tsayar da tsohon mataimakin gwamna Manir Dan’iya bayan taron tattaunawa a tsakanin masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar suka yi, a inda aka cimma nasarar tsayar da Manir a matsayin dan takara a jam’iyyar ADC a 2027.
Daga karshe, Manir Dan’iya, ya kara tabbatar da godiyarsa ga tsohon kakakin majalisar tarayya kuma Sanata mai ci a yanzu, Aminu Waziri Tambuwal, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC bisa tsayar da shi a bisa cancantarsa.
Trending
- Gobarar Singer: ‘Yan kasuwa sun nemi gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka
- Months after Singer market fire, affected traders demand fulfilment of government support promises
- Radda launches $1m food security project to tackle floods, drought
- Shuaibu Dan Saurayi: How Hausa digital content is giving young creators a voice
- Governor Idris applauds ongoing reforms at NAHCON
- Plateau flags off education support vehicles, materials to strengthen basic education
- Lalong joins Plateau APC leaders in reconciliation efforts ahead of 2027
- 23rd National Sports Festival: Zonal eliminations for team sports set for September 12–15


