Daga Ahmad Ibrahim Gusau
Majalisar Dokokin Jahar Zamfara karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, a zaman ta na majalisa, ta tattauna tare da amincewa da tsawaita dakatarwar da ta yi wa mambobi bakwai na majalisar zuwa karin wa’adin zangon majalisa guda daya.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Zamfara, Bello Madaro Kurya, ya fitar, ana binciken ‘yan majalisar ne bisa zargin aikata rashin da’a da karya dokokin gudanarwar majalisa.
Wannan matsaya ta biyo bayan kudurin da Jagoran Masu RinJaye na Majalisar, Hon. Bello Muhammad Mazawajje ya gabatar tare da samun goyon bayan Hon. Ibrahim Garba Liman (Fegin Mahe), mai wakiltar mazabar Gusau II.
Yayin gabatar da dalilan tsawaita dakatarwar, Hon. Bello Muhammad Mazawajje ya bayyana cewa, duk da cikar wa’adin dakatarwar farko, ci gaba da shari’ar da ake yi kan lamarin ya sanya dole a tsawaita matakin ladabtarwar har sai kotu ta yanke hukunci.
Bayan cimma matsaya baki daya daga mambobin majalisar, Kakakin majalisar Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki ya sanar a hukumance da tsawaita dakatarwar mambobin da abin ya shafa da suka hada da Hon. Bashir Abubakar mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Arewa da Hon. Bashir Aliyu mai wakiltar Gummi I, da Hon. Nasiru Abdullahi mai wakiltar Maru.
Sauran sun hada da Hon. Faruku Musa Dosara mai wakiltar Maradun I, Hon. Amiru Ahmad Keta mai wakiltar Tsafe West, Hon. Ibrahim T. Tukur mai wakiltar Bakura, da Hon. Bashir Bello mai wakiltar Bungudu.
Trending
- Namadi Dala distributes motorcycles to loyalists
- Sokoto upgrades, renames college after Wamakko
- A Zamfara: Majalisar dokoki ta tsawaita wa’adin dakatar da ‘ya’yanta 7
- Ƙaramar hukumar Bichi ta karrama ɗalibai da jami’an ilimin yankin
- A Bichi: Abubakar Kabir Abubakar ya ciri tuta a zaɓen fitar da gwani
- Cross River cleric condemns Obubra communal clash, alleges over 50 killed
- 2027: Governor Yusuf backs Abba Bichi’s re-election bid
- NDC extends deadline for Expression of Interest Forms to May 24
