Daga Yusuf Abdullahi Muhammad

Shugabancin Kainuwa Youth Association dake yankin Gama ya bayyana cewa ziyarar da wasu mutane suka kai wa Dan Takarar Majalisar Tarayya na Karamar Hukumar Nassarawa, Hon. Mustafa Alkassim (Danhajiya), ba ta samu amincewar kungiyar ba, kuma ba ta wakilci matsayar kungiyar ba.

Kungiyar ta ce mutanen da suka gudanar da ziyarar sun yi amfani da sunan kungiyar ba tare da izini ko sahalewar shugabancinta ba, lamarin da ta bayyana a matsayin cin amanar amana da kuma saba wa dokokin kungiyar.

Shugabancin kungiyar ya jaddada cewa babu wani mataki na siyasa ko wata ziyara da za a gudanar da sunan kungiyar sai da amincewar shugabannin da ke kan mulki.

Kungiyar ta bukaci al’umma da su yi watsi da duk wani bayani da ke nuna cewa ita ce ta shirya ko ta amince da wannan ziyara.

Wadanda suka sanya hannu:
Usman Usman Garba – Sakataren Kungiya (Secretary)

Ibrahim Tijjani – Jami’in Hulɗa da Jama’a (Public Relations Officer)

Musa Abba – Mukaddashin Shugaban Kungiya (Acting Chairman)

An fitar da wannan sanarwa ne domin fayyace matsayar kungiyar da kuma kare mutuncinta daga duk wani amfani da sunanta ba tare da izini ba.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version