Daga Abdulbaki Ali Ahmad Sharifai

Kungiyar Cigaban Matasan Unguwar Kundila (KUYODA) da ke karamar hukumar Tarauni a Jihar Kano, ta kaddamar da sabuwar cibiyar koyar da sana’o’in hannu domin tallafa wa matasa maza da mata wajen samun dogaro da kai.

Bikin bude cibiyar wanda aka gudanar a harabar makarantar firamare ta Kundila, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na Jihar Kano, ciki har da ‘yan siyasa, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.

Da yake jawabi yayin taron, shugaban kungiyar KUYODA, Barr. Nasir Ado, ya bayyana cewa kafa wannan cibiya wani muhimmin mataki ne wajen samar wa matasa hanyar samun sana’a da kuma kau da su daga zaman banza da miyagun dabi’u.

Ya ce cibiyar za ta taimaka wajen bai wa matasa maza da mata dabarun sana’o’i domin su zama masu amfani ga kansu, iyalansu da kuma al’umma baki daya.

Barr. Nasir ya gode wa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin an cimma nasarar wannan shiri.

A nasa jawabin, dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Tarauni, Hon. Dahiru Sule (ADS), ya jaddada muhimmancin samar da ayyukan yi ga matasa, inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin da suka shafi rashin aikin yi.

Dan majalisar, wanda shi ne ya kaddamar da cibiyar, ya tallafa wa cibiyar da gudunmawar Naira miliyan daya.

Haka kuma, dan majalisar wakilai mai wakiltar Tarauni a Majalisar Tarayya, Hon. Mukhtar Umar Yarima, ya yi alkawarin bai wa cibiyar cikakken goyon baya domin cimma manufofinta.

Hon. Yarima, wanda sakataren kudi na jam’iyyar NDC a Kano, Hon. Engr. Shamsuddeen, ya wakilta, ya ce zai tallafa wajen horas da matasa tare da samar musu da jari domin fara sana’o’in da za su koya.

Shi ma Engr. Shamsuddeen ya yi alkawarin amfani da kwarewarsa a fannin kere-kere wajen taimaka wa cibiyar da horo na musamman, inda ya bayar da gudunmawar Naira miliyan daya.

Haka kuma, dan takarar majalisar wakilai mai wakiltar Tarauni a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Nasir Aminu Ja’oji, wanda Hon. Ali PRS ya wakilta, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan daya ga cibiyar.

Tun da farko, daya daga cikin iyayen unguwar Kundila, Mai Shari’a Maryam Ahmad Sabo, ta jaddada muhimmancin hadin kai, taimakon juna da kuma kokarin zama sanadiyyar sauya rayuwar wasu zuwa hanya mai kyau.

Justice Maryam Ahmad Sabo ta kuma tallafa wa cibiyar da gudunmawar Naira dubu dari biyu.

An bayyana cewa cibiyar za ta mayar da hankali wajen koyar da matasa sana’o’i daban-daban domin bunkasa tattalin arziki da samar da masu dogaro da kai a cikin al’umma.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version