Daga Rabiu Sanusi

Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyuka da kuma Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kawo sauyi mai ma’ana a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar Kano.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilinmu a Kano, Rabiu Sanusi, Namadi Dala ya ce ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa sun sauya fasalin Kano tare da inganta rayuwar jama’a.

Haka kuma ya bayyana cewa Jam’iyyar APC za ta ci gaba da samun goyon bayan al’umma idan ta ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi ci gaban kasa.

Tambaya:
Da farko, yaya kuke kallon nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu zuwa yanzu?

Namadi Dala:
Da farko ina taya Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar nasarorin da ya samu a wannan lokaci da ya shafe yana jagorantar Kano. Gaskiya gwamnatin sa ta kawo sauyi mai ma’ana a fannoni da dama. An samu ci gaba a ilimi, lafiya, hanyoyi, samar da ruwa, sufuri da sauran muhimman bangarori da suka shafi rayuwar al’umma.

Tambaya:
Kun taba rike Ma’aikatar Bibiyar Ayyuka ta Jihar Kano. Mene ne kuka gani game da ayyukan gwamnatin?

Namadi Dala:
A lokacin da nake wannan ma’aikata, mun bibiyi ayyuka sama da 2,000 da gwamnati ta gudanar a sassan jihar Kano. Wannan ya nuna irin jajircewar gwamnatin wajen tabbatar da cewa ci gaba ya kai ga kowane yanki na jihar.

Tambaya:
Wane bangare ne kuke ganin ya fi samun ci gaba a wannan gwamnati?

Namadi Dala:
Gaskiya kusan dukkan bangarori sun samu ci gaba. A bangaren ilimi an gyara makarantu tare da tallafawa dalibai. A bangaren lafiya an inganta asibitoci da samar da kayan aiki. Haka kuma an gudanar da manyan ayyukan hanyoyi da sauran ayyukan more rayuwa da suka amfani jama’a.

Tambaya:
A matsayinka na tsohon Kwamishinan Sufuri da Bibiyar Ayyuka, yaya kake kallon ci gaban da aka samu a wannan fanni?

Namadi Dala:
An samu gagarumin ci gaba. An gudanar da ayyuka masu yawa da suka taimaka wajen inganta harkokin sufuri a Kano. Wasu daga cikin ayyukan ma hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya.

Tambaya:
Kana yawan magana kan makomar Kano. Yaya kuke hasashen jihar a shekaru masu zuwa?

Namadi Dala:
Ina da yakinin cewa Kano na tafiya ne zuwa wani sabon matsayi na ci gaba. Idan aka ci gaba da irin wadannan ayyuka, Kano za ta kasance cikin manyan biranen da suka fi bunkasa a Najeriya da ma Afirka baki daya.

Tambaya:
Yaya kake kallon shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa?

Namadi Dala:
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zo da manufofi da shirye-shirye da dama domin bunkasa tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar jama’a. Duk wani gyara yana bukatar lokaci kafin a ga cikakken amfaninsa, amma akwai alamun cewa wadannan shirye-shirye za su haifar da kyakkyawan sakamako a nan gaba.

Tambaya:
Shin kana ganin wadannan shirye-shirye za su taimakawa APC a zabuka masu zuwa?

Namadi Dala:
Hakika. Idan jama’a suka ci gaba da ganin amfanin wadannan tsare-tsare da ayyukan ci gaba, babu shakka APC za ta kara samun karbuwa a fadin Najeriya. Ayyuka su ne babban hujjar neman goyon bayan jama’a.

Tambaya:
Ka taka muhimmiyar rawa a yakin neman zabe da ya gabata. Mene ne sirrin nasarar APC a Kano?

Namadi Dala:
Sirrin nasara shi ne kusanci da jama’a. Tun daga matakin mazabu har zuwa karamar hukuma da jihar baki daya, muna tare da jama’a kuma muna sauraron bukatunsu. Wannan ne ya sa APC ta kasance jam’iyyar da ke da karfi sosai a Kano.

Tambaya:
Wace gudunmawa kake shirin bayarwa a zabuka masu zuwa?

Namadi Dala:
Zan ci gaba da amfani da gogewata wajen hada kan ‘ya’yan jam’iyya, karfafa tsarin jam’iyya da kuma wayar da kan jama’a. Ina da yakinin cewa tare da hadin kai da aiki tukuru za mu samu nasara a zabuka masu zuwa.

Tambaya:
Wane sako kuke da shi ga al’ummar Kano?

Namadi Dala:
Ina kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zaman lafiya da goyon bayan ayyukan ci gaba. Kano jiha ce mai dimbin albarka da dama, kuma idan muka hada kai za mu kai ta matakin da kowa zai yi alfahari da ita.

Tambaya:
A karshe, yaya kake kallon makomar Kano da Najeriya?

Namadi Dala:
Ina da kwarin gwiwa cewa makomar Kano da Najeriya mai kyau ce. Tare da shugabanci nagari, hadin kai da jajircewa wajen aiki, za mu ga karin ci gaba da bunkasar tattalin arziki a shekaru masu zuwa.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version