Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

Kungiyar Matasan Arewa maso Yamma (NYUF) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin kawo karshen tashe-tashen hankula da zubar da jini da ake fama da su a jihohin Arewa maso Yamma cikin kwanaki 30.

Kungiyar ta bayyana cewa idan ba a samu gagarumin ci gaba wajen magance matsalar tsaro ba a cikin wa’adin da ta bayar, mahalarta taronta za su dauki duk wata hanyar da ta dace domin neman a hukunta masu hannu a cikin wadannan munanan ayyuka.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Murtala Ishaqa Jangebe, ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A cewar sanarwar, kungiyar ta nuna matukar damuwa kan ci gaba da kashe-kashe, garkuwa da mutane, fyade, satar shanu da kuma korar al’umma daga matsugunansu a yankin Arewa maso Yamma.

Kungiyar ta ce wadannan matsaloli sun jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa, tare da tilasta wa daruruwan al’ummomi barin gidajensu domin neman mafaka a manyan birane ko kuma hedikwatar kananan hukumomi.

NYUF ta kuma bayyana cewa hanyoyin da ke hada jihohin yankin ba su da cikakken tsaro, lamarin da ya sanya zirga-zirga da harkokin kasuwanci cikin hadari.

Sanarwar ta kara da cewa mafi yawan al’ummomin yankin na rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren masu aikata laifuka, wanda ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na tsaro da tattalin arziki.

Bugu da kari, kungiyar ta bukaci gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Jigawa, Sokoto, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi da Zamfara da su gaggauta daukar jami’an tsaron gandun daji 2,000 a kowace jiha, tare da samar musu da kayan aiki da makaman da suka dace domin yaki da ta’addanci da sauran munanan laifuka.

Kungiyar ta jaddada cewa daukar wadannan matakai na da matukar muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version