Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a harkokin ta’addanci tare da kwato makamai daban-daban a wani samame da ta kai a yankin Kasuwar Daji da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Yazid Abubakar, ya fitar, ya bayyana cewa jami’an sashen yaki da laifukan ta’addanci sun gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 29 ga Mayu, 2026.
Sanarwar ta ce wadanda aka kama sun hada da Ali Bahago, Hassan Dan Kure da Dahiru Lawali, dukkansu mazauna yankin Kaura Namoda.
Binciken farko ya nuna cewa suna da alaka da wata kungiyar masu aikata laifuka da ake zargin Ali Bahago ke jagoranta, wanda ya dade yana cikin jerin sunayen mutanen da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo.
A yayin samamen, jami’an tsaro sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargin tare da kwato makamai da suka hada da bindigar famfo guda daya, bindigar ganga guda daya, wata bindigar G3 da aka kera cikin gida, bindigogin Dane, alburusai da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka.
Rundunar ta ce ana ci gaba da tsare wadanda ake zargin domin fadada bincike, gano sauran mambobin kungiyar da kuma kwato karin makamai.
Ta kuma sake jaddada kudirinta na yaki da miyagun laifuka a fadin jihar tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
