Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Alhaji Hamza Musa Mai Bulawus ya zama dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Zamfara, bayan ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ba tare da hamayya ba.
An gudanar da zaben fidda gwanin ne ta hanyar kai tsaye a dukkan gundumomi 147 da ke cikin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara, inda ‘ya’yan jam’iyyar suka kada kuri’unsu domin amincewa da dan takarar.
A sakamakon zaben, an bayyana cewa Mai Bulawus ya samu kuri’u 36,556, wanda ke nuna cikakkiyar goyon baya daga mambobin jam’iyyar a fadin jihar.
Da yake sanar da sakamakon zaben a Gusau a ranar Talata, jami’in da ke kula da zaben fidda gwani na SDP daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa, Bello Hussaini Gusau, ya ce an gudanar da aikin cikin tsari da bin doka.
“Bisa ikon da aka ba ni a matsayina na jami’in dawo da sakamakon zaben fidda gwani na gwamna a SDP, na ayyana Hamza Musa Mai Bulawus a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani a jihar Zamfara,” in ji shi.
Nasarar da ya samu ba tare da hamayya ba ta tabbatar da cewa Hamza Musa Mai Bulawus zai wakilci jam’iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Zamfara na shekarar 2027.
Jam’iyyar SDP ta bayyana cewa an shirya zaben fidda gwanin ne kai tsaye domin tabbatar da halartar mambobi daga sassan jihar, tare da ƙarfafa haɗin kai gabanin babban zaɓe.
