Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da ware naira miliyan 460.83 domin tallafa wa mata masu kananan sana’o’i, ciki har da masu tuyan kosai da sauran ‘yan kasuwa kanana a mazabu 178 da ke fadin jihar.
Amincewar na daga cikin kudurorin da Majalisar Zartarwa ta Jihar ta cimma a zamanta da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a Fadar Gwamnati da ke Damaturu.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Al’adu, Alhaji Abdullahi Bego, ya ce an dauki matakin ne domin karfafa tattalin arzikin mata masu kananan sana’o’i ta hanyar samar musu da kayan aikin da za su inganta harkokinsu.
Ya bayyana cewa majalisar ta amince da kashe naira miliyan 460,828,450 domin sayen wake da za a raba wa mata masu sana’o’i a matsayin tallafin bunkasa kasuwancinsu.
A cewarsa, wadanda za su amfana za su samu buhunan wake tare da man girki, murhun zamani maras hayaki, kayan girki da kayan kicin, wadanda Ma’aikatar Samar da Arziki, Karfafawa da Samar da Ayyukan Yi ta riga ta sayo tare da adanawa.
Bego ya kara da cewa za a raba buhunan wake 1,780 masu nauyin kilo 50 ga wadanda aka zaba domin cin gajiyar shirin.
Hakazalika, ya ce majalisar ta kuma amince da ware naira miliyan 364.475 domin sayen injunan nika nau’in Yamaha GX 390 guda 1,000, wadanda za a raba wa masu anfani a sassan jihar domin inganta sana’o’insu.
Baya ga haka, kwamishinan ya bayyana cewa majalisar ta amince da gudanar da ayyuka da darajarsu ta kai naira biliyan 73.32 a muhimman bangarorin tattalin arzikin jihar.
Ya ce ayyukan sun hada da naira biliyan 28.53 domin sayen kayan aikin noma a karkashin Shirin Karfafa Manoma na shekarar 2026, naira biliyan 23.97 domin manyan ayyukan hanyoyi guda biyu, da kuma wasu kudade na ayyukan gidaje, kasuwanni da sauran muhimman ababen more rayuwa.

