Musa lemu daga Sakkwato
A ranar Litinin 11 ga Mayu, 2026, jirgin farko na maniyyata aikin hajjin bana su 485 suka tashi daga Sakkwato zuwa kasa mai tsarki domin gudunar da ayyukan ibada.
Jirgi mai suna Aquline mallakar Umza zai doshi birnin Madina a inda maniyyatan za su fara gudunar da ibada kafin zuwa birnin Makka, maniyyatan da suka fito daga kananan hukumomi Tambuwal, da Tureta da Wamakko da Sabon Birni da Isa da Shagari da kuma Dange Shuni.
A yayin da yake jawabin ban kwana ga maniyyatan, gwamna Ahmad Aliyu , wanda mataimakinsa Injiniya Idris Muhammad Gobir ya wakilta, gwamnan ya tabbatar wa maniyyatan cewa , gwamnatin jihar Sakkwato ta samar da dukkan abubuwan da suka dace ga maniyyatan a kasa mai tsarki.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ce, an san al’ummar Sakkwato da tsare doka da mutunci a ko’ina suka sami kansu. Ya shawarce su da su kasance jakadu nagari tare da gudanar da addu’o’i ga jihojin da ke cikin tarnaki a kan matsalar tsaro.
Da yake jawabin bankwana ga maniyyatan, Amirul Hajji na wannan shekara 2026 , Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, wanda shi ne ministan kwadogo, ya yi fatan samun nasara a bisa jigilar maniyyatan.
Ana sa ran cewa, maniyyata 2,404 za su sauke farali a bana, a inda jirgin zai jigilar maniyyatan sawu 5 kacal daga Sakkwato.
Muhammadu Maigari Dingyadi, wanda shi ne Katukan Sakkwato, ya kuma nanata cewa , maniyyatan su tabbatar sun bi dokokin Saudi Arabiya kamar yadda dokar kasa ta shinfida .
Daga karshe, ya gamsu da dukkan shirye shirye da aka gudanar a filin jirage na Sultan Abubakar na 3 da ke Sakkwato.

