Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen Jihar Yobe ta sanar da Lawan Mohammed Kori a hukumance a matsayin mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2027, wanda zai yi takara tare da dan takarar gwamna, Kassim Gana Gaidam.
An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin jam’iyyar daga yankunan majalisar dattawa uku na jihar, inda aka kafa kwamitin mutum biyar domin tantance wadanda suka dace da mukamin mataimakin dan takarar gwamna.
Kwamitin, karkashin jagorancin Babban Mai Binciken Kudi na Kasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Mai Adamu Mustapha, ya kunshi Abdulhamid Buba, Alhaji Yahaya Bukar, Alhaji Umar Kalli da Alhaji Mamu Muhammad.
A cewar jam’iyyar, kwamitin ya yi amfani da ka’idoji da suka hada da cancantar ilimi, gogewar siyasa, biyayya ga jam’iyya da kuma karbuwar dan takara a tsakanin al’umma wajen gudanar da tantancewar.
Bayan kammala aikinsa, kwamitin ya mika shawarwarinsa ga dan takarar gwamna, Kassim Gana Gaidam, wanda daga bisani aka amince da Lawan Mohammed Kori a matsayin mataimakin dan takarar gwamna.
Lawan Mohammed Kori fitaccen dan siyasa ne wanda ya taba wakiltar mazabar tarayya ta Nangere/Potiskum a Majalisar Wakilai daga shekarar 2007 zuwa 2011.
Jam’iyyar ta bayyana cewa an zabe shi ne bisa biyayyarsa ga jam’iyyar, gogewarsa da kuma goyon bayan da yake samu daga jama’a.
A cikin wata sanarwa, Sakataren Jam’iyyar ADC na Jihar Yobe, Dr. Mamu Muhammad, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar su mara wa sabon tikitin jam’iyyar baya, yana mai cewa jam’iyyar ta kuduri aniyar samar da zaman lafiya, ci gaba da wadata ga al’ummar Yobe.
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana kwarin gwiwarsu cewa haduwar Kassim Gana Gaidam da Lawan Mohammed Kori za ta kara wa ADC karfi yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni na shekarar 2027.

