Daga Rabiu Sanusi
Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na mazaɓar Gezawa da Gabasawa Alhaji Rabi’u Yusuf Danmalam ya buƙaci magoya bayansa da al’ummar yankin da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri, biyayya ga doka da oda tare da rungumar ƙaddara yayin da ake jiran umarnin gwamnati kan mataki na gaba.
Danmalam ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro da ya gudanar da masu ruwa da tsaki, shugabannin matasa dattawa da wakilan mazaɓu daban-daban daga ƙananan hukumomin Gezawa da Gabasawa.
A cikin jawabin nasa, Alhaji Rabi’u Yusuf Danmalam ya nuna matuƙar godiya da irin goyon baya, addu’o’i da jajircewar da magoya bayansa suka nuna masa tun farkon tafiyarsa ta siyasa har zuwa wannan lokaci.
Ya bayyana cewa duk da yadda al’amura suka kasance a halin yanzu, lokaci ne da ke buƙatar haƙuri, hikima da kuma biyayya ga shugabanni domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Danmalam ya jaddada cewa duk wani mataki da za a ɗauka dole ne ya kasance cikin lumana tare da bin tanade-tanaden doka.
“Mun rungumi ƙaddara, kuma muna kira ga magoya bayanmu su ma su rungumi ƙaddara tare da jiran umarnin gwamnati. Duk wani abu da za mu yi dole ne ya kasance cikin lumana da bin doka,” in ji Danmalam.
Ya ƙara da cewa siyasa wata hanya ce ta hidimtawa al’umma da samar da ci gaba, ba wai ta rikici ko tayar da tarzoma ba. Haka kuma ya yi kira ga matasa da su guji duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar yankin.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka gabatar da nasu jawaban sun bayyana cikakken goyon bayansu ga jagorancin Alhaji Rabi’u Yusuf Danmala, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da nuna haƙuri da biyayya har sai an bayyana mataki na gaba.
Masu jawabin sun bayyana Danmalam a matsayin jagora mai kishin al’umma, mai mutunta jama’a da fifita zaman lafiya da haɗin kai a dukkan harkokinsa na siyasa da zamantakewa.
Taron ya gudana cikin lumana da fahimtar juna, inda aka gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban mazaɓun Gezawa da Gabasawa baki ɗaya.

