Daga Rabi’u Sunusi
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci daurin auren gata na zawarawa da ’yan mata 1,500, ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar da Hukumar Hisbah ta Kano ta gudanar.
Gwamnan ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin tsari na jin ƙai da tallafa wa al’umma, wanda ke da nufin dawo da fata, ƙarfafa zaman iyali da kuma inganta kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
Ya ce shirin ya nuna ƙudirin gwamnatinsa na rage wa marasa galihu nauyin da ke tattare da aure, tare da samar da damar kafa iyali cikin mutunci, bisa koyarwar addinin Musulunci da kyawawan al’adun Hausawa.
A yayin gudanar da daurin auren, Gwamna Yusuf ya wakilci angon farko, inda ya nemi auren amaryar daga hannun waliyyinta, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, wanda ya amince da buƙatar bisa tanadin addinin Musulunci.
Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano ya gabatar da hudubar Juma’a, inda ya shawarci sabbin ma’auratan da su gina zamansu bisa imani, haƙuri, mutunta juna da tausayi, yana mai jaddada cewa zaman lafiyar iyali shi ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce an tantance dukkan waɗanda suka amfana da shirin, tare da tabbatar da cika dukkan sharuɗɗan addini da na doka kafin gudanar da daurin auren.
Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, ya jagoranci addu’o’in neman shiriya, albarka da zaman lafiya ga sabbin ma’auratan.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan gagarumar gudunmawa, inda suka bayyana cewa shirin ya ba su damar fara sabuwar rayuwa cikin mutunci da kyakkyawan fata.
Shirin auren gata na daga cikin manufofin Gwamnatin Jihar Kano na bunƙasa walwalar al’umma, ƙarfafa zaman iyali da inganta zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

