Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

Jam’iyyar Action Alliance (AA) reshen jihar Zamfara ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Aare Adekunle Rufai Omoaje, wanda ya faru a wajen wani taron jana’iza a ranar Asabar.

Jam’iyyar ta bayyana harin a matsayin farmaki kai tsaye kan dimokuraɗiyya da kuma ‘yancin gudanar da siyasa cikin lumana.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a yammacin ranar Lahadi a Gusau, Shugaban AA na jihar Zamfara, Alhaji Shehu Hussaini Waziri, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata harin tare da gurfanar da su gaban shari’a.

Ya ce: “Jam’iyyar Action Alliance ta jihar Zamfara na Allah wadai da wannan mummunan hari da aka kai wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Aare Adekunle Rufai Omoaje, wanda ya faru a ranar Asabar a wajen taron jana’izar da aka gudanar a Ekusa, ƙaramar hukumar Odo Otin ta jihar Osun.”

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version