By Shafi’u Yahaya

Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah na Karamar Hukumar Kumbotso, Sheikh Mudansir Auwal, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da taimaka wa marasa ƙarfi tare da jajircewa wajen aikata ayyukan alheri, musamman a cikin goman farkon watan Zulhijja.

Sheikh Mudansir Auwal ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Karamar Hukumar Kumbotso.

Ya ce wannan lokaci na goman farko na Zulhijja lokaci ne mai albarka da ya kamata Musulmi su yi amfani da shi wajen ƙara kusanci ga Allah ta hanyar ibada da ayyukan taimakon jama’a.

Ya bukaci masu hali da sauran al’umma da su tallafa wa mabukata da marasa galihu domin samun lada da kuma inganta zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, lafiya, nasara da jagoranci nagari wajen gudanar da harkokin jihar.

Ya kuma yi wa Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Hardworker, fatan alheri da nasara a ayyukansa na ci gaban al’umma.

A ƙarshe, Mataimakin Kwamandan Hisbah ya yaba wa Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Kumbotso bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da kyawawan ɗabi’u, zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version