Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta dage sauraron karar da dan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya shigar kan kalubalantar sahihancin zaben fidda gwani da ya haifar da fitowar Sanata Sahabi Ya’u Kaura a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Mai shari’a Hassan Dikko ya jagoranci zaman kotun, inda kotun ta lura da rashin halartar biyu daga cikin wadanda ake kara, wato APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Saboda haka, kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yunin 2026, domin tabbatar da cewa an yi wa dukkan wadanda ake kara isar da sammaci yadda doka ta tanada tare da ba su damar gabatar da martaninsu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, lauya mai kare wanda ake kara na uku, Barr. J. C. Shaka, ya bayyana cewa ya halarci zaman kotun kuma ya gabatar da bukatar a yi watsi da karar.

Ya ce babu wani zaben fidda gwani na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa da wanda yake karewa, Sanata Sahabi Ya’u Kaura, ya yi nasara a cikinsa kamar yadda mai karar ke ikirari.

A nasa bangaren, lauya mai wakiltar mai kara, Barr. Bello Galadi, ya ce kotun ta dage sauraron karar ne zuwa ranar 25 ga Yuni domin bai wa sauran wadanda ake kara damar bayyana a gaban kotu tare da gabatar da matsayinsu kan lamarin.

Galadi ya jaddada cewa suna ci gaba da neman adalci dangane da zaben fidda gwanin da ya samar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura a matsayin wanda ya lashe tikitin APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.

“Har yanzu muna nan kan bakarmu ta neman adalci a gaban kotu game da zaben fidda gwanin sanatoci wanda ya samar da wanda ake kara na uku a matsayin wanda ya yi nasara.

Muna ganin zaben ya kasance cike da kura-kurai da kuma saba ka’idojin da suka tanadi yadda ya kamata a gudanar da shi,” in ji Galadi.

Kotun za ta ci gaba da sauraron karar a ranar 25 ga Yuni, 2026.

Share.
Leave A Reply

Join Us On WhatsApp
Exit mobile version